Wata mata na zargin Conor McGregor da cin zarafinta

Ana zargin McGregor ya turmushe matar a makewayi.

Wata mata na zargin Conor McGregor da cin zarafinta

Masu shigar da kara a Amurka sun fara tuhumar fitacccen dan damben UFC, Conor McGregor da zargin cin zarafin wata mata a lokacin da ake wasan karshe na gasar kwallon Kwando ta NBA birnin Miamin Amurka cikin watan nan.

Wata wasika da aka aike wa McGregor ta yi zargin cewa dan damben ya bi wata mata har makewayi a cibiyar Kaseya tare da cin zarafinta lokacin da ake wasan na karshe, ko da ya ke lauyansa ya musanta zargin.

Lauyan na McGregor ya ce ba za su amince da bata sunan dan damben ba.

Tuni dai Ofishin ‘yan sanda na Miami ya bude bincike kan zargin da ake yi wa fitaccen dan damban, yayin da kwamitin gudanarwa na UFC ya bayyana cewa yana sane da zargin kuma ya fara bincike don tattara hujjoji.

Lauyar matashiyar da ke zargin McGregor da cin zarafinta, Ms Ariel Mitchell ta bayyana cewa matashiyar na tsaka da kallon wasan karshe na ranar 9 ga watan nan ne lamarin ya faru.

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa