Wata mata ta ƙone kanta a Jigawa

Bincike ya nuna cewa matar ta shiga damuwa tun bayan mutuwar aurenta.

Wata mata ta ƙone kanta a Jigawa

Wata mata mai shekara 40, Fatsuma Bagobiri ta banka wa kanta wuta a ƙauyen Garin Mallam da ke Ƙaramar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin.

DSP Shiisu ya ce an samu rahoton faruwar lamarin ne a safiyar ranar Alhamis, kuma jami’an ofishin ‘yan sanda na shiyyar Guri sun gaggauta kai wa matar ɗauki.

Ya ce jami’an sun kai matar asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta kuma daga bisani aka miƙa ta ga iyalanta domin yi mata jana’iza.

Binciken farko da aka yi ya nuna cewa marigayiyar ta shiga cikin damuwa tun bayan rabuwar aurenta a watannin baya.

Kwamishinan ‘yan sandan Jigawa, CP AT Abdullahi, ya buƙaci jama’a da su riƙa miƙa al’amuransu ga Allah Ta’ala, su yi addu’ar neman albarka, da kuma neman shawara a wajen manya a kan al’amura masu sarƙaƙiya.

Ya ce irin wannan mummunan yanayi da ake tsintar kai a cikin ya sanya yake da mahimmancin a rika duba lafiyar kwakwalwa da kuma neman taimakon makusanta.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta