Wata mata ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa

Wata mata ta antaya wa kisihyarta tafasasshen ruwa bayan wata takaddama da ta kaure a tsakaninsu. Aika-aikan ya samo asali ne bayan kishiyoyin biyu, Ikilim da Justina sun yi wata jayayya a tsakaninsu amma, mijinsu mai suna, Ate Peter Manomi ya raba rikicin suka tsagaitawar husumar. Wata mata ta cire wa kishiyarta kunne da cizo […]

Wata mata ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa

Matar da kishiyarta ta watsa mata tafasasshen ruwa

Wata mata ta antaya wa kisihyarta tafasasshen ruwa bayan wata takaddama da ta kaure a tsakaninsu.

Aika-aikan ya samo asali ne bayan kishiyoyin biyu, Ikilim da Justina sun yi wata jayayya a tsakaninsu amma, mijinsu mai suna, Ate Peter Manomi ya raba rikicin suka tsagaitawar husumar.

Jim-kadan sai Iklima ta fito daga dakinta da kayanta na wanki, kafin ta ankar Justina ta kai mata farmaki da tafasasshen ruwa ta antaya mata.

Saman jikin Ikilima ya sassale sakamakon tafasasshen ruwan da Justina ta antaya mata.

Mijin matan da makwabta sun shiga cikin tashin hankali da takaici saboda da danyen aikin da Justina ta yi wa amaryar tata wacce yanzu take jinya.

Aminiya ta gano cewa Justina ta saba rikici da amayar tata tun lokacin da mijinta ya auro Iklima kimanin shekara uku da suka gabata.

“Ina kwasan kayana da na wanke ne, ban yi zaton kishiyar tawa ta nufo ni da wani mugun nufi ba.

“Ban yi zaton komai makamancin wannan ba, saboda an riga an raba mu bayan mun yi fada ’yan mintoci kafin hakan ta faru. Ina mikewa ke nan sai kwara min tafasasshen ruwa, sai na fara ihu ina neman dauki,” inji Iklima

“Mijinmu ne ya fara gaggawar shigowa inda abun ya faru. An yi sa’a bai yi nisa da gida ba, ya jiyo ihuna. Ban san iya abun da zai iya faruwa ba da ba ya kusa.”

Tuni maigidan ya garzaya da Iklima zuwa asibiti, inda aka kwantar da ita a Asibitin Kwararru na Sabon Layi da ke Mangu.

Rikicin tsakanin kishiyoyin ya sa Iklima barin gidan a watan Agustan 2019, ba ita ta dawo ba sai a 2020 da tunanin cewa zuwa lokacin Justina ta huce.

“Abin mamaki ranar dana dawo ta biyo in har dakina tana da fadar bakaken maganganu,  muka yi cacar baki har muka ba hamata iska, lokacin ne na fahimci cewa da sauran rina a kaba,” kamar yadda ta ce.

Zuwaira Haruna Marwe, ita ce mahaifiyar Iklima, ta ce ita da ma ba ta gamsu da shawarar komawar Iklima gidan Manomi ba saboda yawan rikice-rikicen da ake samu.

“Ina Legas lokacin da lamarin ya faru. Bayan kwana daya da faruwar abun ’yar uwarta ta kirawo ni a waya cewa Iklima ba lafiya, suna asibiti sakamakon kunar dake jikinta,” inji mahaifiyar Iklima.

Ta ci gaba da cewa kafin hakan ta faru an taba zuba wa Iklimma wani abu a cikin ruwan wankanta, wanda ya illata fatarta. Wanda likita Ikliman ya ce guba aka zuba mata a cikin ruwan.

Lamarin da ya faru da ’yar tata iklima a kwana-kwanan nan ya fusata Zuwaira cikin zullumi da fargaba.

“Ni uwa ce, na damu da abun da ya faru. Justina ta cutar da ’yata tana kuma neman halaka mun ita. Babbar bukatata ita ce a yi mana adalci, a kuma tabbatar da t agirbi abun da ta shuka,”inji ta.

Kawun Iklima, Marwe Abdulganiyu Abubakar, ya ce hankalinsa ya tashi da ganin halin da ya gan ta a ciki Asibiti.

Ikilima ta ce ba za ta yafe ba, sai idan har kishiyar tata ta gamsar da ita cewa ba ta zuba mata tafasasshen ruwan da nufin cutar da ita, saboda a cewarta, a baya Justina ta sha cutar da ita.

Duk da halin da Iklima ta shiga da raunin da ke jikinta ta yarda cewa aurenta na nan kuma da zarar ta warke za ta ci gaba da zama da mijinta.

“Na gamsu cewa mijina na so na ni ma kuma ina son shi. Idan har zai raba mana gida to zan iya ci gaba da zama da shi amma idan hakan ba ta samu ba bana jin zan iya komawa gidan na ci gaba da zama da Justina,” inji Iklima.

Mijin nasu, Manomi, ya kasa cewa uffan kan lamarin, yayin da wakilin Aminiya ya nemi magana da shi.

“Wannan lamari ne da ya shafi iyali kuma ba na son nace uffan a kai.”

Barnabas Zumji, jami’in dan sanda ne a ofishin rundunar ’yan sanda na Gindiri, ya ce sun samu labarin abun da ya faru kuma da zarar Iklima ta warke za su yi mata tambayoyi da za su taimaka wurin binciken lamarin, yayin da suke ci gaba da bincike kan lamarin a halin yanzu.

Tun lokacin da lamarin ya faru, Justina ta tsere ba a gan ta ba, a gefe daya kuma Iklima da ’yan uwanta sun ci gaba da tuntubar ’yan sanda  kan yadda za a yi a ganta a kuma gurfanar da ita a gaban kotu.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro