Wata mata ta ce Sheikh Inyas ya bayyana a dakinta
A tsakar ranar shekaranjiya Laraba ce dubban jama’a suka rika yin tururuwa zuwa Unguwar Tullukawa da ke Gusau fadar Jihar Zamfara bayan da suka samu labarin cewa Sheikh Ibrahim Nyas ya bayyana a jikin bangon dakin wata mata a unguwar.Wakilinmu wanda ya halarci unguwar domin gano gaskiyar abin da ya faru ya gano cewa a […]

A tsakar ranar shekaranjiya Laraba ce dubban jama’a suka rika yin tururuwa zuwa Unguwar Tullukawa da ke Gusau fadar Jihar Zamfara bayan da suka samu labarin cewa Sheikh Ibrahim Nyas ya bayyana a jikin bangon dakin wata mata a unguwar.
Wakilinmu wanda ya halarci unguwar domin gano gaskiyar abin da ya faru ya gano cewa a ranar Talata ce matar mai suna Halimatus Sa’adiyya ta ce ta fara ganin Shehin ne a bangon dakinta, sai ta yi sauri ta bayyana wa wadanda suke zaune tare a gidan, kuma hakan ya sa sauran mutanen suka yi kokarin duba inda matar ta ce Shehin yana fitowa.
Wata majiya ta ce, mutanen sun gan shi sanye da alkyabba da rawani da carbi.
Malam Muhammad Nazifi da ke zaune a gidan, a zantawarsa da Aminiya ya ce lokacin da aka gaya masa ya yi mamaki, amma koda ya je ya duba sai shi ma ya ce Allah Ya yi masa ludufi da ganin Shehin, kuma tun yana fitowa a bangon cikin dakin sai ya zama har a waje don haka duk wadanda suka je a ranar Talata duk sun gan shi, inji malamin.
Malam Muhammad Nazauma shi ne ke da gida da aka ce Shehin ya bayyana, a zantawarsa da wakilinmu ya ce tun yana zaune a gidansa akazo aka bayyana masa, amma har abin ya wanzu kowa ya ji, ya ce saboda wannan ko da mutane za su rugurguza gidan ne ba ya da damuwa don Shehi ya bayyana a gidansa. Ya kara da cewa wadanda suke shakka kan wannan wasu sun koma suna bakin ciki wasu kuwa suna farin ciki. Ya ce batun gini kuwa Allah zai maida masa da abinsa.
Abdullahi Abubakar Mairake ya bayyana wa wakilinmu cewa ya je ya ga shehi a inda ya bayyana, kuma ya san ba shi Shehin ba ne ya so ya bayyana, a’a ya ce ubangijinsa ne Ya so ya yi haka kuma ya yi a wannan lokaci, kuma ita wadda aka ga Shehin a dakinta jika ce ga Malam Muhammad Nazoma.
Malam Abubakar ya ce ya ga Shehin da idanunsa cikin rawani da alkyabba da carbi yana kishingide, kamar an haska majigi. Shi kuma Malam Buhari Musa ya ce ya samu labari ne sakamakon ganin wasu suna wucewa, wannan ya sa ya tambaya, kuma ya ce ya dauki tsawon lokaci bai gan shi ba, sai bayan ana ta yin zikiri, sannan ya bayyana ya samu ganinsa.
Shi kuwa Malam Mu’azu wanda ya ce ya samu ganinsa, ya bayyana wa wakilinmu cewa ba kowa ba ne ke samun ganinsa ba, don wasu da yawa an yi ta nuna musu amma ba su gan shi ba.