Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas
“Yan sanda a halin yanzu suna binciken al’amuran da suka shafi mutuwar matar.”

An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunanta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas.
Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas.
- Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo
- Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar
“Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas kuma likitocin jami’ar UNILAG sun tabbatar da mutuwarta a gaban rundunar ’yan sanda daga sashin Sabo,” kamar yadda sanarwar a wani ɓangare ta bayyana.
Hundeyin ya ci gaba da cewa, an kai gawar zuwa ɗakin ajiye gawarwaki na Asibitin cututtuka masu yaɗuwa da ke yankin Yaba a jihar domin adanawa.
Ya ƙara da cewa “Yan sanda a halin yanzu suna binciken al’amuran da suka shafi mutuwar matar.”