Wata mata ta gano macizai 18 a kasan gadonta
Muna fata an fitar da macizan duka.
Wata mata ta tsallake rijiya da baya bayan da ta gano wata macijiya ta kyankyashe ’ya’ya 17 a karkashin gadonta a daidai lokacin da take shirin yin barci.
Matar mai suna Trish Wilcher wadda take zaune a Jihar Jojiya ta kasar Amurka, ta ce ta kadu sosai lokacin da ta gano macizan a dakinta.
- Har yanzu ina sa ran zan fita Kasar waje — Rabi’u Ali
- Rahoton Sahara Reporters ya fusata dubban musulmai
Bayanai sun ce matar ta rika tunanin kila akwai sauran macizan duk da wani kwararre a kan macizan ya fitar da su daga dakin.
Kafafen labarai ciki har da Sky.News sun ce matar ta ga alamar wani gashigashi yana motsi a cikin dakinta, kuma da ta kura ido sai ta gano maciji ne.
Daga baya sai ta sake ganin wani yana motsi a kasa. Daga karshe ta gano macijiyar da ’ya’yanta 17 bayan ta wargaza gadonta.
Misis Wilcher ta ce tana zargin macijiyar ta haihu ne a karkashin gadon a ranar Lahadin makon jiya.
Wasu hotuna sun nuna yadda ake iya hango macizan wadanda suka saje da kafet din dakin.
Wannan lamari ya jefa matar a cikin ‘firgici’ da ‘razana’ kamar yadda ta bayyana a shafinta na facebook.
Ta rubuta cewa: “Mun wargaza dakin… mun gano ’ya’yan macizai 17 da uwarsu.
“An share wani fili a can bakin hanya wanda ciyayi da itatuwa suka girma a cikinsa sosai… don haka babu mamaki hakan ya sa macijiyar ta gangaro gidanmudon samun mafaka!”
“Har yanzu ina tunanin barin gidan domin duk lokacin da na zauna a ko’ina a ciki ina firgice.
“Ina jin akwai bukatar likitan zuciya ya duba ni,” Misis Wilcher ta fadi a cikin raha.
Wani da ya mayar mata da martani a shafin na facebook yana yi mata godiya kan yadda aka fitar da macizan cikin karramawa.
Misis Wilcher ta amsa da cewa: “Muna fata an fitar da su duka – amma har yanzu ina ji a jikina cewa akwai saura a dakin.”
“Duk da mun daina tsoron barazana bayan gano uwar macizan… amma har yanzu ina dar-dar, har yanzu ban gama sakin jiki da gidan ba.”
Wani kwararre kan dabbobi mai suna Dan ne ya fitar da macizan ya kai su wata korama da take kusa a garin Augusta.
Ta ce: “Dan ya zo ya tafi, bai sake gano wani ba… ina zargin macijiyar ta haihu ne a karkashin gadona… eh a karkashin gadona! Har yanzu ina cike da kaduwa.”
Misis Wilcher ta ce macizan ba masu dafi ba ne. An ce macizan masu ruwan kasa ne ko launin rawaya wadanda ba masu dafi ba ne.