Wata mata ta haifi ’yan biyar a Jamhuriyar Czech

Wata mata ’yar kasar Czech, mai shekara 23, ta haifi maza hudu da mace daya. Matar wadda aka yi wa lakabi da uwar ’ya’ya ko “Supermum” ta samu taimakon ma’aikatan asibiti a kalla 40, wadanda suke kwararru ne a sashin kula da lafiyar masu juna biyu na asibitin Prague-Podoli, inda suka yi mata tiyata a […]

Wata mata ta haifi ’yan biyar a Jamhuriyar Czech
Wata mata ta haifi ’yan biyar a Jamhuriyar Czech

Wata mata ’yar kasar Czech, mai shekara 23, ta haifi maza hudu da mace daya. Matar wadda aka yi wa lakabi da uwar ’ya’ya ko “Supermum” ta samu taimakon ma’aikatan asibiti a kalla 40, wadanda suke kwararru ne a sashin kula da lafiyar masu juna biyu na asibitin Prague-Podoli, inda suka yi mata tiyata a mako na 31 da ta yi tana rainon ciki. Kafafen yada labarai sun bayyana sunan matar da , Aledandra Kinoba.
 “Wannan yarinyar sunanta Tereza, su kuwa sauran tagwayen mazan sunayensu, sun hada da Michael da Deniel da Aled da Martin,” a cewar mahaifinsu dan shekara 26, mai suna Antonin Krosen, kamar yadda ya sanar da manema labarai.
“Ina cike da farin ciki,” inji shi.
Wadannan jrirai dai an dauki cikinsu, an kuma yi goyon cikin bisa ka’idar zamantakewar iyali. Sai dai yanzu ana ba su kula ta musamman a wani sashe na musamman a asibitin da mahaifiyarsu ta haihu.
“A kasarmu, tun daga shekarar 1949 kididdigar bincike ta nuna ba a taba haihuwar ’yan hudu ba. A jamhuriyar Czech ana haihuwar ’yan biyar a bayan kowace shekara 480,” a cewar likitan lafiyar masu juna biyu, Alena Mechuroba.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda