Wata mata ta haifi ’yan biyar a Katsina

Hajara Shuaibu ta haifi ’yan biyar baan ta haifu tagwaye sau biyu

Wata mata ta haifi ’yan biyar a Katsina

Jarirai

Wata mata ta haifi ’yan biyar a kauyen Doma da ke Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina.

Mai jegon, mai suna Hajara Shuaibu, ta haifi ’yan biyar din ne a ranar Larabar ko da ake daga bisani Allah Ya yi wa biyu daga cikinsu (mace da namiji) rasuwa, sauran ukun kuma na cikin koshin lafiya.

Binciken Aminiya ya gano a gida Hajara ta haifi wasu daga cikin yaran, kafin daga baya aka garzaya da ita Babbar Asibitin Funtuwa inda a nan ta haifi sauran ukun.

Mahaifin Hajara ya ce daga Asibitin Funtuwa sai aka tura su Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina don ci gaba da samun kulawa.

Ya kara da cewa a baya, ’yarsa Hajara ta haifi tagwaye har sau biyu inda wannan karon kuma ta haifi ’yan biyar.

Ya ce wannan shi ne karon farko a tarihin kauyensu inda aka samu wata ta haifi ’yan biyar.

Shi kuwa mijin Hajara, Shuaibu Hussein, ya bayyana farin cikinsa da wannan baiwa da Allah Ya yi musu, amma ya nuna damuwa kan yadda za su yi fama da dawainiyar yaran kasancewarsu masu karamin karfi.

Don haka ya yi kira ga gwamnati da hukumomi masu zaman kansu da sauran masu hannu da shuni da su taimaka musu game da dawainiyar kula da yaran.

Ko a kwanan nan, an samu wata da ta haifi ’yan biyar kamar Hajara a Umuahia, babban birnin Jihar Abia, mai suna Oluomachi Lynda.

Gobara ta ƙone shaguna 50 a kasuwar kara a Sakkwato

An yi canjaras tsakanin Liverpool da Manchester United

Tinubu zai tafi Ghana rantsar da John Mahama

’Yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah na Katsina, sun sace iyalansa