…Wata mata ta haifi ’yan-hudu
A ranar Talatar makon da ya gabata ne wata mata mai shekara 24 mai suna Maimuna matar Muddassiru Bala ta haifi jarirai mata guda hudu a gida mai lamba 20 layin Iyawe Crescent, Aduwawa, Benin. Matar da mijin nata duk ’yan asalin karamar Hukumar Gusau ne ta Jihar Zamfara.Muddassiru Bala ya ce sun shekara biyar […]
A ranar Talatar makon da ya gabata ne wata mata mai shekara 24 mai suna Maimuna matar Muddassiru Bala ta haifi jarirai mata guda hudu a gida mai lamba 20 layin Iyawe Crescent, Aduwawa, Benin. Matar da mijin nata duk ’yan asalin karamar Hukumar Gusau ne ta Jihar Zamfara.
Muddassiru Bala ya ce sun shekara biyar ke nan da matarsa, wadda ita ce ta fari kuma haihuwarta ta farko namiji ne mai suna Ja’afaru, sai ta biyu mace mai suna Sa’adiyya, daga nan sai wannan da ta haifi ’yan hudu.
Malam Muddassiru ya ce, “Ina cike da farin ciki, kuma na gode wa Allah, domin ba ta taba haihuwa a cikin sauki irin haka ba, karewa ma a gida ta haihu ba tare da wata wahala ba.”
Wakilin Aminiya ya ziyarci asibitin Modic Medical Center, inda likitoci ke kulawa da jariran har zuwa lokacin da za su sami kwarin ji sosai, kafin a sallame su. Babban likita, Dokta Dominic Osaghae tare da mataimakiyarsa Dokta Zuwo sun tabbatar da cewa dukkan jariran suna cikin koshin lafiya tare da mahaifiyarsu.
Mahaifiyar ’yan-hudun ta ce, “Ina gode wa Allah tare da fata Ya raya su cikin koshin lafiya, domin ban taba tunani zan samu ko da ’yan-biyu ba balle ’yan hudu. Allah Ya albarkace su”.