Wata mata ta haifi ’ya’ya 14 da maza 14 daban-daban
Wata mata mai shekara 36 a Jihar Michigan ta kasar Amurka ta kafa tarihi bayan ta haihu a asibitin Koyarwa na Jami’ar Harper, inda ta haifa danta na 14, amma kuma kowanne dan da mahaifinsa daban. A wani binciken kididdiga da aka gudanar, an gano cewa Anita Sulliban ita ce mace ta farko da ta […]
Wata mata mai shekara 36 a Jihar Michigan ta kasar Amurka ta kafa tarihi bayan ta haihu a asibitin Koyarwa na Jami’ar Harper, inda ta haifa danta na 14, amma kuma kowanne dan da mahaifinsa daban.
A wani binciken kididdiga da aka gudanar, an gano cewa Anita Sulliban ita ce mace ta farko da ta haifa wa sama da maza 13 ’ya’ya, wanda hakan ke nuni da cewa an taba samu mata da ta haihu da maza har 13, amma ba a taba samun wadda ta haihu da maza 14 ba a tarihin duniya.
A cewarta, “Ina matukar farin ciki da jin dadin yadda na kafa wannan tarihi,” inji Anita Sulliban, lokacin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan ta haihu a asibitin.
“Mahaifiyata ta sha fada min cewa ina da kasala da yawa, kuma wai ba zan tabuka komai ba a rayuwata ta duniya ba, amma yanzu duniya ta gani cewa ta yi kuskure, domin yanzu duniya ta shaida cewa zan iya dagewa in yi duk abin da na yi niyyar aikatawa. Hasali ma na yi abin da ba a taba yi ba a tarihi yanzu haka.”
Anita Sulliban ta kara da cewa ba ta samu nasarar ko kuma jin dadin soyayya ba a baya, amma tana tunanin yanzu ta samu wanda ya dace da ita.
“Ina da kokarin haihuwa, amma ina da rauni wajen zaben uban ’ya’yana wanda za mu zauna da shi mu ci gaba da rayuwa.
“Amma yanzu ina tunanin na gane kuskurena, yanzu na samu wanda zai yi daidai da mutumin da nake so in ci gaba da zama da shi. Ramon mutumin kirki ne ba kamar sauran mashirmanta da suke neme ni a baya ba. Yanzu haka mun shafe kusan shekara daya da rabi da shi, kuma ina tsammanin za mu ci gaba da zama da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya,” inji ta.
Bayan samun labarin ta haifi da na 14 daga maza daban-daban, sai masu naziri da rubuta abubuwan mamaki wato Guiness record suka fara bincike a kan ko akwai wadda ta taba samun irin wannan matsayi, amma ba su samu ba, wanda hakan ya sa aka tabbatar mata da tarihin.