Wata mata ta jefa ’ya’yanta biyu a rijiya saboda kuncin rayuwa
Dawowa ta Najeriya ce ta jefa ni cikin kuncin rayuwa.
Wata mata a ranar Talata ta jefa ’ya’yanta biyu mata cikin rijiya a yankin Ibuaje da ke Osogbo, babban birnin Jihar Osun.
Mazauna yankin sun bayyana cewa kuncin rayuwa da matar ta tsinci kanta na gaza dawainiya da yaran biyu ya sanya ta aikata wannan danyen aiki.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce “matar ta fara jefa babbar ’yar ce mai shekara bakwai sannan ta jefa karamar mai shekara biyar da misalin karfe 2.00 na rana.”
Har ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, yaran biyu suna cikin rijiyar a yayin da jami’an Hukumar Kwana-Kwana na Jihar Osun ke kokarin ceto su.
Mai magana da yawun hukumar kwanan-kwanan, Mista Ibrahim Adekunle, ya ce rijiyar tana da kogo 24 sannan a cike take makil da ruwa.
Sai dai ya ce jami’ansu na ci gaba da fafutikar ganin sun ceto yaran biyu.
Da take bayani cikin sambatu, mahaifiyar yaran ta ce tana zaman cirani ne a ketare kuma daga bisani aka taso keyarta wanda hakan ya jefa ta cikin matsin rayuwa a Najeriya.
Wasu al’ummar yankin sun shaida wa wakilinmu cewa, akwai yiwuwar ta zauce saboda halin kunci da ta shiga bayan an dawo da ita Najeriya.