Wata mata ta kai wa magidanci hari a ofishin ’yan sanda
Mutumin ya samu raunuka a jikinsa, gami da fargabar rasa rayuwarsa.
An gurfanar da wata mata mai shekara 50 a gaban kotu kan laifin kai wa wani mutum farmaki a cikin ofishin ’yan sanda a Abuja.
Dan sanda mai gabatar da kara SP Babajide Olanipekun ya shaida wa kotun da ke Kuba a Abuja cewa, abin da matar ta yi mutumin ya haifar masa da masa raunuka a jikinsa, da kuma jefa shi cikin firgici da barazanar rasa rayuwarsa.
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Muke Yin Ciko —’Yan Mata
- Mako 1 da juyin mulkin Nijar: Faransa ta fara kwashe ’yan kasarta
Ya bayyana wa alkali cewa wadda ake tuhumar ta yi wa mutumin wannan aika-aika ne ta hanyar watsa masa abu mai ruwa-ruwa a cikin ofishin ’yan sandan yankin a ranar 17 ga watan Yuli, 2023.
Sai dai matar ta musanta zargin da ake mata, bayan dan sandan ya ja hankalin kotu cewa abin da ta aikata laifi ne a dokar Penal Code.
A karshe dai alkalin Babbar Kotun, Malam Yahaya Sheshi, ya ba da belin wadda ake zargin a kan kudi N500,000 da kuma mutum daya da zai tsaya mata, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Agusta.