Wata mata ta kashe ’ya’yan saurayinta a Binuwai

Lamarin ya faru ne da safiyar Litinin bayan matar ta yi zargin cewa saurayinta yana tare da wata mata a cikin wani ɗaki.

Wata mata ta kashe ’ya’yan saurayinta a Binuwai

Wata mata mai suna Mbayegh na hannun ’yan sanda bisa zargin haddasa gobarar da ta yi sanadin mutuwar ’ya’ya mata biyu na saurayinta a garin Zaki-Biam da ke Ƙaramar Hukumar Ukum a Jihar Binuwai.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da safiyar Litinin bayan matar ta yi zargin cewa saurayinta yana tare da wata mata a cikin wani ɗaki.

Sai dai, a cewar mazauna yankin, saurayin ba ya cikin ɗakin a lokacin, kuma ’ya’yansa biyu ne kawai ke barci a ciki.

An ce yaran, Precious Ordo mai shekara shida da Sember Ordo mai shekara huɗu, sun maƙale a cikin gobarar.

Ɗaya ta rasu nan take, yayin da ɗayar ta rasu daga baya a asibiti sakamakon raunukan da ta samu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Binuwai, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa gobarar.

’Yan sandan sun bayyana cewa an kama wata mata da ake zargi kuma tana taimaka wa masu bincike.