Ta tsare ma’aikatan banki da ‘bindiga’ domin kwashe kudin ajiyarta

Wata mata ta kutsa cikin banki dauke da bindiga inda ta tsare ma’aikata tare da tilasta musu ba ta kudinta da take ajiya.

Ta tsare ma’aikatan banki da ‘bindiga’ domin kwashe kudin ajiyarta

Wata mata ta tsare ma’aikatan banki da bindiga bayan an hana ta cire kudi daga asusun ajiyarta na Dala domin kula da lafiyar ’yar uwarta.

A ranar Laraba matar, sanye da bakaken kaya da fuskarta a bude ta shiga BLOM Bank da ke Beirut, babban birnin kasar Lebanon, ta yi wa kanta wanka da man fetur, tana barazanar kona kanta da bankin, idan ba a ba ta kudin ajiyarta ba.

Kan ka ce kwabo, ma’aikatan banki da kwastomomi reshen bankin da ke Sodeco suka fara kyarma suna ihu; kafin daga baya wasu kwastomomi su fasa gilasan bankin suka samu suka tsere.

Matar, wadda ke tare da ’yan rakiya,  ta bukaci bankin ya ba ta Dala 20,000 da ke asusun hadin gwiwarta da kanwarta mai shekara 23 da ke fama da cutar kansar kwakwalwa.

Babu shiri ma’aikatan bankin suka yi ta harhado dalolin da ke ajiye a wurinsu, da kyar samu aka ba ta Dala 13,000 ta tafi tare da ’yan rakiyarta.

Ta shiga bankin ne bayan ta fito daga hedikwatarta tsaron kasar tare da ’yan rakiyarta, ciki har da wani lauya da kuma masu rajin kare hakkin masu ajiya a banki.

Bayan bankin ya ba ta kudinta, sai suka tafi, tare da magoya bayanta; bayan isowar jami’an tsaro, suka tsinci bindigar da matar ta yar, wadda suka gano cewa ta roba ce.

Wata ma’aikaciyar Bankin BLOM tana nuna gilashin da kwastomomi suka fasa a garin turereniyar tserewa daga cikin bankin. (Hoto: AP)

Jami’an tsaro sun tsare wasu daga cikin masu fafutikar da ke zanga-zanga a kusa da bankin domin nuna adawa ga Shugaban Babban Bankin kasar.

Daga baya wani gidan talabijin ya yi hira da ita, inda ta bayyana cewa ita ba barauniya ba ce ko ’yar fashi, dole ne ya sa ta yi abin da ta yi domin ceto rayuwar ’yar uwarta.

Ta ce, “’Yar Uwata na bukatar a yi mata allura mai tsada a kullum, amma kwana biyu kafin yau na je bankin na gaya musu halin da muke ciki, amma suka ce Dala 200 kawai za su iya ba ni a wata.

“Duk abin da muka mallaka mun sayar da shi, har kodata na so in sayar domin samun kudin jinyar jinyar kanwata.

“Kudin da ke asusun ajiyar, ni da ita muka tara daga aikin da muke yi.”

Ta ce hasali ma duk abin da ta yi an dauka a bidiyo domin kafa shaida, kuma babu wanda ta cutar don haka bai kamata a zarge ta da sata ko fashi ba.

Ta kara da cewa, “A cikin kayan wasan daya daga cikin ’ya’yan ’yan uwana na dauko bindigar robar.”

Amma hukumar gudanarwar bankin na zargin cewa an kitsa abin da matar ta yi ne da nufin cutarwa.

Tun da farko a ranar Labarar dai, irin haka ta faru a yankin Aley na kasar ta Lebanon.

Gwamnatin kasar Lebanon dai ta sanya wa masu ajiyar Dala takunkumi kan cire kudi, sakamakon matsalar kudi da kasar ta jima tana fama da ita.

Mutane da dama, musamman masu ajiya a bankunan kasar, wadanda aka hana su cirar kudi daga banki, sun nuna goyon bayansu ga abin da aka yi wa bankunan.

Ko a makonnin baya, Aminiya ta kawo rahoton yadda wani mutum ya shiga wani banki a birnin na Beirut dauke da bindiga ya yi garkuwa da ma’aikata tare da barazanar kashe kansa da kona bankin idan ba a ba shi kudin da yake ajiye a asusunsa na Dala ba, domin biya wa mahaifinsa kudin asibiti.

Hotunan zanga-zangar tsofaffin sojoji Abuja

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 95 a ƙasar Tibet

Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno

Ɗan ta’adda ya sa wa Zamfarawa harajin N100m