Wata matar aure ta sari mijinta da adda 

’Yan sanda sun bayyana cewa a yayin rikicin da ya ɓarke tsakanin ma’auratan, matar ta kai wa mijin hari da adda ta ya masa mummunan rauni a hannun hagu.

Wata matar aure ta sari mijinta da adda 

Wata matar aure da ake zargin ta sari mijinta da adda ta shiga hannun hukuma a Jihar Ondo.

’Yan sanda sun bayyana cewa a yayin rikicin da ya ɓarke tsakanin ma’auratan, matar ta kai wa mijin hari da adda ta ya masa mummunan rauni a hannun hagu.

An garzaya da mijin nata mai suna Olatunde Julius, zuwa asibiti, inda aka duba tare da rubuta irin raunin da ya samu.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Ondo, DSP Abayomi Jimoh, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Yuni, 2026, da misalin ƙarfe 2:30 na dare, yayin hatsaniyar.

Rundunar ta bayyana cewa bayan kammala bincike da kuma tabbatar da akwai isassun hujjoji na fara shari’a, an gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu.

’Yan sanda sun jaddada cewa duk nau’ikan cin zarafin cikin gida na haifar da barazana ga rayuwa, mutunci da walwalar jama’a, tare da sake tabbatar da aniyarsu ta ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifi, ba tare da la’akari da jinsi, matsayi ko dangantaka da wanda abin ya shafa ba.

Haka kuma rundunar ta shawarci jama’a da su rika hanzarta kai rahoton duk wani lamari na cin zarafi da dangoginsa zuwa ofishin ’yan sanda ko hukuma mafi kusa domin ɗaukar matakin gaggawa bisa doka.