Wata matar aure ta shirya sace kanta da kanta a Jihar Enugu
Satar mutane a yi garkuwa da su domin neman kudin fansa, tana ci gaba da daukar sabon salo a yankin Kudu maso Gabas na kasar nan, inda ake zargin wata mace ta shirya sace kanta da kanta domin neman kudin fansa.Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu ce ta damke matar wadda matar aure ce bisa zargin […]

Satar mutane a yi garkuwa da su domin neman kudin fansa, tana ci gaba da daukar sabon salo a yankin Kudu maso Gabas na kasar nan, inda ake zargin wata mace ta shirya sace kanta da kanta domin neman kudin fansa.
Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu ce ta damke matar wadda matar aure ce bisa zargin shirya sace kanta da kanta tana nemi mijinta ya biya kudin fansa kafin a sako ta.
Gidan Rediyon BBC Landan wanda ya ruwaito labarin ya ce matar mai suna Nancy Chuckwu tana zaune ne a karamar Hukumar Ogu da ke Jihar Enugu, kuma ana zarginta ne da hada baki da wani dan acaba da sunan an sace ta an kuma yi garkuwa da ita domin samun kudin fansa daga hannun mijinta.
Gidan Rediyon BBC ya ce satar mutane don neman kudin fansa dai ta zama ruwan dare a Najeriya, musamman ma a Kudancin kasar, kuma babu alamun samun saukin matsalar.
A kwanan baya ma, wani matashi a yankin Kudu maso Gabas ya hada baki da wata mace domin shirya sace kansa da kansa, inda matar ta fada wa danginsa cewa wadanda suka yi garkuwa da shi suna neman a biya su kudin fansa kafin su sako shi.
Har ma danginsa sun fara zuba kudin a asusun ajiyar matar da suka hada baki da matashin, daga bisani ’yan sanda sun bankado shirin, suka kuma kama su.
… matashi ya yanke mazakutarsa a Anaca
Musa Kutama a Awka
Wani matashi mai shekara 30 mai suna Ejike ya gutsure mazakutarsa da wuka a kauyen Nkpor da ke karamar Hukumar Idenmili ta Kudu dab da shiga garin Anaca a Jihar Anambra.
Asali dai shi wannan matashi kamar yadda majiyarmu ta bayyana an ce tsohon yaron manyan motocin nan da ke zirga-zirga daga jihohin Kudu zuwa na Arewa, amma ya yi ritaya ya koma kauye da zama. Majiyar ta ce ashe yana da wata manufa a zuciyarsa sai ya tafi wurin tsafinsu domin neman biyan wata bukata.
Majiyyar ta ce bayan da ya kammala bin duk sharuudda da ka’idojin gidan tsafin ne sai aka ce ya furta tare da fallasa kansa game da irin miyagun ayyukan da ya aikata a baya. Majiyar ta ce a yayin da ke furta irin laifuffukan da ya yi ne, sai ya sanya wuka ya yanke azzakarinsa, kuma yin haka ke da wuya sai aka ga wani kare ya bayyana a gidan ya zo ya dauke su ya arce.
“Yanzu haka yana kwance a wani asibiti mai suna Crown a kauyensu Nkpor yana jinya.
Da aka tuntubi likitan asibitin Dokta Eddy Emegoaku ya gaskata labarin, amma ya ce yana samun sauki. Sai dai kuma likitan ya yi gum da bakinsa lokacin da aka nemi ya yi karin bayani.