Wata matashiya ta hana zaki cinye akuyarta a Indiya

Wata matashiya a Indiya ta tsallake rijiya da baya, bayan ta kori wani zaki da sanda saboda ya kai wa akuyarta hari. Rupali Meshram mai shekara 23, ta ce bayan da ta ji akuyar tana kuka, sai ta yi maza ta ruga ta nufi inda akuyar take a wajen gidansu, inda ta ga ashe zaki […]

Wata matashiya ta hana zaki cinye akuyarta a Indiya

Wata matashiya a Indiya ta tsallake rijiya da baya, bayan ta kori wani zaki da sanda saboda ya kai wa akuyarta hari.

Rupali Meshram mai shekara 23, ta ce bayan da ta ji akuyar tana kuka, sai ta yi maza ta ruga ta nufi inda akuyar take a wajen gidansu, inda ta ga ashe zaki ne ya kai wa akuyarta hari. 

Daga nan ne sai ta dauki sanda ta fara dukan zakin, wanda daga baya kuma ya afka mata kamar yadda BBC ta ruwaito.

Mahaifiyarta wadda ita ma ta samu raunuka, ita ta cece ta ta hanyar ingiza ta cikin gida.

Dukansu dai sun samu raunuka, amma zuwa yanzu an sallame su daga asibiti, sai dai kuma akuyar ba ta rayu ba.

Rupali ta dauki hoton kanta jim kadan da faruwar lamarin a makon jiya a yammacin Jihar Maharashtra, fuskarta duk jini.

Likitan da ya duba ta ya yaba mata sosai, inda ya ce, ta yi namijin kokari da ta tunkari zakin, amma kuma ta yi babbar sa’a da zakin bai cinye ta ba.

Matashiyar dai ta samu raunuka a kanta da kwankwasonta da hannunta, amma tana samun sauki sosai. Sannan ta bayyana alhininta na rasa akuyarta.

Mahaifiyar Rupali ta shaida wa BBC cewa, “Na zaci ’yata za ta mutu saboda yadda na ga tana kokarin ceton kanta da sanda daga hannun zakin da kuma irin jinin da na ga yana zuba daga jikinta.”

kauyen su Rupali dai na kusa da wani daji ne, kuma yana fuskantar barazanar shigar namun daji a kai- a kai. Don haka suke kira ga masu kula da namun dajin da ke kusa da kauyen nasu  da su rika sa ido a kan dabbobin saboda gudun faruwar wani lamari kamar na Rupali.

 

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu