Wata mawakiyar zamani a Maleysiya ta musulunta

Wata fitacciyar mawakiyar zamani ’yar kasar Maleysiya mai suna Stracie Angie Anam da aka fi sani da Stacy AF ta bayyana wa taron manema labarai cewa ta karbi addinin Musulunci.Mawakiyar ta bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata bayan da aka rika yada jita-jitar ta musulunta sakamakon ganinta sanye da hijabi. Stacy AF ta […]

Wata mawakiyar zamani a Maleysiya ta musulunta
Wata mawakiyar zamani a Maleysiya ta musulunta

Wata fitacciyar mawakiyar zamani ’yar kasar Maleysiya mai suna Stracie Angie Anam da aka fi sani da Stacy AF ta bayyana wa taron manema labarai cewa ta karbi addinin Musulunci.
Mawakiyar ta bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata bayan da aka rika yada jita-jitar ta musulunta sakamakon ganinta sanye da hijabi.
 Stacy AF ta fadi a wurin taron manema labarai a dandalin wasa na ta ce: “Eh, na karbi addinin Musulunci jiya (ranar Litinin) kuma ita ce ranar da na fi jin dadi a rayuwata,” kamar yadda kafar labarai ta News Straits Times da ke fitowa a intanet ta ruwaito.
Kafofin sadarwa na intanet sun rika yada jita-jitar cewa Stacy AF wadda ta lashe gasar Akademi Fantasia Season 6 ta musulunta bayan da aka rika yada wani faifan bidiyonta tana karbar Kalmar Shahada tare da sanya hijabi.
Ta karbi Musulunci ne a a ofishin addini na Johor Baru da ke garin Johor inda ta sauya sunanta zuwa Ummu Shyaikha Stacy binti Anam.
“Sai dai har yanzu ina amsa sunan Stacy,” inji mawakiyar wadda iyayenta, Agnes Kaloos, mai shekara 57 da Anam Bayar mai shekara 53, suke tare da ita a lokacin taron manema labaran.
Mawakiyar mai shekara 25 ta yi album din waka hudu, kuma ta ce tana fata masoyanta ba za su tuhumi dalilin musuluntarta ba. “Ni Kirista ce a da, kuma na yi alfahari da haka. To amma wannan batu ne na zuciya, ina matukar kaunar Musulunci kuma na shirya rungumarsa da dukkan karfina, kuma ina fata kowa zai girmama zabina,” inji ta.
Ta musanta rade-radin cewa ta musulunta ne saboda saurayinta wani ma’aikacin talabijin Musulmi mai suna Akim Ahmad, inda ta musanta cewa musuluntarta na da alaka da shirin aure da Ahmad din.
 “Ba gaskiya ba ne. Ni da Akim ba mu da wani shiri na yin aure. In da na musulunta ne do kawai ina son aurensa da sai in bari sai an sanya ranar auren. Kasancewa Musulma wata babbar amana ce. Akwai dimbin abubuwan da suka wajaba in koya. Yanzu abin da na mayar da hankali a kai shi ne in koyi yadda zan zama Musulma tagari kafin in fara tunanin yin aure,” inji ta.
A nasa bangare, Ahmad ya nuna bacin rai kan yadda aka rika yayata bidiyon musuluntar Stacy ba tare da izininta ba. “Idan kana girmama wani to ka daina yada bidiyon ka share wanda aka dauka ba tare da izini ba,” ya rubuta a shafinsa na Tweeter kamarb yadda jaridar Rakyat Post ta ruwaito.
Ya kara da cewa: “Ku girmama abin da ya shafi rayuwar mutum, bai kamata a rika yayada sirrin wani ba.”
Stacy ta ce bayan yayata hoto da bidiyon jikinta ya yi sany saboda ba da izininta aka yi hakan ba. Ta ce “Ba wai ina kokarin boye wannan labari mai dadi ba ne, amma lamari ne da ya shafe ni, saboda wasu daga cikin dangina ba su san na musulunta ba. Yaya kuke jin za su ji idan suka hoto da bidiyon musuluntata?”  Ta ce ta so a bar ta ta sanar da su da kanta a hankali maimakon a dauka a watsa ba tare da sani ko izininta ba. “A matsayina na sabuwar Musulma na yafe mata, (wadda ta yayata musuluntar)” inji ta.