Wata minista a Birtaniya ta yi murabus saboda rikicin Gaza

Minista ta farko mace Musulma a gwamnatin Birtaniya Sayeeda Warsi ta yi murabus a ranar Talatar da ta gabata bayan da ta zargi gwamnatin Dabid Cameron da gazawa kan tsawatar wa Isra’ila a yakin da take a yankin zirin Gaza wanda kuma ta ce yana zubar wa da kasar kima a idon duniya.Murabus din wanda […]

Wata minista a Birtaniya ta yi murabus saboda rikicin Gaza
Wata minista a Birtaniya ta yi murabus saboda rikicin Gaza

Minista ta farko mace Musulma a gwamnatin Birtaniya Sayeeda Warsi ta yi murabus a ranar Talatar da ta gabata bayan da ta zargi gwamnatin Dabid Cameron da gazawa kan tsawatar wa Isra’ila a yakin da take a yankin zirin Gaza wanda kuma ta ce yana zubar wa da kasar kima a idon duniya.
Murabus din wanda ya zo wa sauran manyan ministocin gwamnatin da mamaki, wani koma baya ne ga gwamnatin Firaminista Cameron dangane da rikicin da ke faruwa a yankin Gabas-ta-tsakiya bayan sukar da yake sha daga bangaren jagoran jam’iyyar adawa ta Labour Ed Miliband kan kauda kai a kisan fararen hular  da ke Gaza.
Firaministan wanda a lokacin murabus din yake bulaguro a kasar Portugal, ya bayyana takaici matuka. Ya kuma ce ya so da ya zanta da ministan gabanin murabus din da ta yi a matsayin  minista a Ofishin Harkokin Waje da kuma Ma’aikatar Addini da ayyukan Al’umma.
A wani sako da ya aika mata ta shafinsa na Tiwita, firaministan ya ce abun da yake faruwa a zirin Gaza abu da ba za a lamunta ba. Kuma gwamnatinsa na goyon bayan baiwa Falasdinawa damar kafa kasar kansu.
 A wani martani da ta fidda daga bisani, ministar ta ce “ba za ta iya aiki da gwamnatin ba saboda manufofinta kan Gaza.”
Shugaban Baitul Malin kasar George Osborne ya bayyana murabus din da wani abu da bai kamata ba.
Minista Sayeeda wadda iyayenta ’yan asalin kasar Pakistan ne, an haife ta ne a yankin arewacin Ingila. Kuma ta kasance wani babban misali da ke nuni da yadda jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta Conserbatibe ta fara canza ra’ayinta inda ta baiwa wadanda ake wa kallon baki kujerar ministan.