Wata Sabuwa: Auren G-Fresh Al-Ameen da Sadiya Haruna na nan daram

Auren Taurarin Tiktok Sayyada Sadiya Haruna da G-Fresh Al-Ameen  Kano state material na nan daram ba kamar yadda ake ta yayatawa ba. A ranar 16 ga Yunin da ya wuce ne aka ɗaura auren shahararrun masoyan na TikTok. Jim kaɗan bayan tarewar Ango a gidan Amarya kuma sai ta tafi aikin Hajji a ƙasa mai […]

Wata Sabuwa: Auren G-Fresh Al-Ameen da Sadiya Haruna na nan daram

Auren Taurarin Tiktok Sayyada Sadiya Haruna da G-Fresh Al-Ameen  Kano state material na nan daram ba kamar yadda ake ta yayatawa ba.

A ranar 16 ga Yunin da ya wuce ne aka ɗaura auren shahararrun masoyan na TikTok.

Jim kaɗan bayan tarewar Ango a gidan Amarya kuma sai ta tafi aikin Hajji a ƙasa mai tsarki.

Matata ce ta sa ni bidiyon barkwanci – Bello Galadanci

Yadda ta kacame tsakanin ’yan TikTok da King Indara

Wannan ta sa kullu yaumin ango G-Fresh ba ya rabuwa da yin bidiyon sambatun shauƙin rabuwa da amaryarsa.

Kwatsam bayan dawowar amarya sai ga labari ya cika TikTok da sauran kafafen soshiyal midiya cewa wai auren taurarin biyu ya mutu.

Har ma wasu ƴan TikTok na cewa wai Gfresh ya yaji ne daga gidan Sayyada Sadiya ya koma kwanan shago bayan da aka samu saɓani a tsakaninsu.

To wai me ya  faru?

Binciken Aminiya ya gano cewa har yanzu Al-ameen G-fresh Kano state material ya na nan a ɗakin Sayyada Sadiya Haruna.

Kuma aurensu na nan igiya uku cif.

Iyakar abin da ya faru shi ne Sayyada Sadiya ta mayar da shafinta na TikTok wurin tallata magunagunan gargajiya da take sayarwa.

Don haka ta goge duk wani bidiyon kwalta da ta yi a baya.

Ciki kuwa har da bidiyoyin soyayyarsu da Kano state material.

Wanann ya sa in ji majiyarmu, ƴan gaza-gani suke yaɗa cewa ko dai aure ya mutu ko kuma ba sa tare.

Sai dai majiyarmu ta ce ma’auratan na shirin fitar da sanarwa idan maganganun ba su tsaya ba.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara