Wata ta auri kanta

Wata mata da ta gaji da zama babu aure, har tsawon shekara shida, sai kawai ta yanke shawarar auren kanta. Duk da cewa kanta ta aura, ta yi shirye-shiryen bikin auren tamkar na ma’aurata. Wannan mata mai suna Grace Gedler ta nuna matukar damuwarta kan zaman da take yi a Landan ba tare da aure […]

Wata ta auri kanta
Wata ta auri kanta

Wata mata da ta gaji da zama babu aure, har tsawon shekara shida, sai kawai ta yanke shawarar auren kanta. Duk da cewa kanta ta aura, ta yi shirye-shiryen bikin auren tamkar na ma’aurata. Wannan mata mai suna Grace Gedler ta nuna matukar damuwarta kan zaman da take yi a Landan ba tare da aure ba, har na tsawon shekaru.
A cewarta, wannan aure ya sa ta samu kwarin gwiwa tamkar dai ba ita kadai take zaune ba. A lokacin bikin, kwaye da abokai, mutum 50 ne suka halarci bikin Grace, inda suka rika kallon Grace tana ta sumbatar kanta a cikin madubi.
Wannan mata ta bayyana cewa: “Mutane kadan ne suka yi sharhi, game da bikin. Tabbas, idan mace tabayyan cewa ta auri kanta, wannan na nuni da son kai, to ni dai ban san yadda al’amarin ya kasance da ni a hakan ba.
Amma dai na samu kwarin gwiwa. Na fara samun bunkasar tunani, na yi rawa na more,don kara fahimtar da kaina yadda al’amura ke faruwa.”