Wata ta haifi ’yan uku a Jihar Katsina

Wata mata mai suna Fa’iza Kabir, ’yar kimanin shekaru 30 da ke garin Fago, karamar Hukumar Sandamu a Jihar Katsina; ta haifi ’ya’ya uku rigis kuma duk mata.Kamar yadda mijinta, Malam Kabir ya ce: “Lokacin da nakuda ta kama ta, mun yi kokarin zuwa babban asibitin Daura, bayan mun je ne, har an fara sayo […]

Wata ta haifi ’yan uku a Jihar Katsina
Wata ta haifi ’yan uku a Jihar Katsina

Wata mata mai suna Fa’iza Kabir, ’yar kimanin shekaru 30 da ke garin Fago, karamar Hukumar Sandamu a Jihar Katsina; ta haifi ’ya’ya uku rigis kuma duk mata.
Kamar yadda mijinta, Malam Kabir ya ce: “Lokacin da nakuda ta kama ta, mun yi kokarin zuwa babban asibitin Daura, bayan mun je ne, har an fara sayo wasu magunguna; to abu ga mai karamin karfi, tun a lokacin ne na fara samun matsala. Ita dai ga yanayin da take ciki, karshe dai sai aka ce aiki za a yi mata, domin fitar da abin da ke cikinta saboda ba za ta iya haihuwa da kanta ba.
“To na fito neman gudunmawa, inda na tuntubi wani Alhaji Ma’azu Fago domin ya yi mini hanya zuwa gidan Sarki da wajen karamar hukuma domin samun tallafi, amma sai ya ce mini, tuni aka bar bayar da irin wannan gudunmawa a masarauta, sai dai ya buga waya karamar Hukumar Sandamu; inda ya ce ga wani mutum nan da aka haifa wa ’yan uku, a ba shi Naira dubu goma,” inji shi.
 Mahaifin yaran ya ce har zuwa lokacin da Aminiya ta tattauna da shi, mai jegon tana cikin wani hali, domin ta sha wuya kwarai amma babu yadda zai yi. A cewarsa, duk da cewa yana da mata uku, bai taba samun haihuwar koda ’yan biyu ba balle ’yan uku ba. “Duk dan abin da na tanada ya tafi tun daga batun magani da farko har zuwa yi mata aiki, ga shi kuma yanzu tana gida amma tana fama da jiki.”
Lokacin da Aminiya ta tuntubi mai jego Fa’iza irin yadda ta ji tun farko kafin yi mata wannan aiki, sai ta ce: “Wannan ita ce haihuwata ta hudu, ban taba jin irin abin da na ji a lokacin da nake dauke da cikin nan ba, musamman irin laulayin da ake ji. Gaskiya na fuskanci abubuwa da dama wadanda ba zan iya tunawa da su ba.”
Sai dai kuma Fa’iza ta nuna farin cikinta duk kuwa da irin halin da take ciki a kan wannan baiwa da Allah Ya ba ta. Ta kara da cewa ita yanzu babbar matsalarta ita ce yadda za ta shayar da su saboda ba ta da isasshen ruwan nono, amma ta ce bangaren jikinta tana samun sauki.
Ita kuwa A’isha wadda take yaya ce ga Kabir, ta ce an taba haihuwar ’yan biyu a gidansu don haka wannan haihuwar ba ta ba su mamaki ba. An yi radin suna ga yaran, inda aka samu Maryam, Hauwa’u da kuma Khadija.