Wata ta sayar da tagwayenta don biyan bashi da sayen sabuwar wayar salula

Bayan biciken da ’yan sanda suka gudanar sun kama wata uwa a kasar China, wadda ta sayar da tagwayen jariranta  kan Dalar Amurka  9,100 (kimanin Naira miliyan 3 da dubu 285 da 100) don ta  biya bashin da ake bin ta sannan ta sayi sabuwar wayar salula samfurin smart phone. A cewar jaridar China Ningbo […]

Wata ta sayar da tagwayenta don biyan bashi da sayen sabuwar wayar salula

Bayan biciken da ’yan sanda suka gudanar sun kama wata uwa a kasar China, wadda ta sayar da tagwayen jariranta  kan Dalar Amurka  9,100 (kimanin Naira miliyan 3 da dubu 285 da 100) don ta  biya bashin da ake bin ta sannan ta sayi sabuwar wayar salula samfurin smart phone.

A cewar jaridar China Ningbo Ebening News, matar wadda ake kira da sunan mahaifinta wato Ma, tana da shekara 20 ta sayar da tagwayen jariran ne, saboda tsananin bashi da takura da take ciki. Mahaifiyar jariran ta ce, ta sayar da jariran ne saboda ta same su ne ba ta hanyar aure ba, ba ta son yaran su girma ba tare da suna ganin mahaifinsu ba, inda ta bayyana cewa mahaifin jariran mai suna Wu, ya fada mata cewa bai bukatar ’ya’yan da ta haifa.

Abin mamaki ne yadda Ma, ta yi kokarin samun masu sayen jariran da ta haifa wata daya kacal. Amma kafar labarai ta ZaoBao ta bayyana cewa, ’yan sandan sun bankado haka ne lokacin da suke wani bincike mai alaka da irin wannan sai suka gano yadda ake gudanar da cinikin jariran, bayan sun tsaurara bincike sai ’yan sandan suka gano an riga an sayar da jariran ga wadansu ma’aurata biyu a Lardin Anhui, masu suna Fuyang da Suzhou a kan Naira miliyan 3 da dubu 285 da 100.

Rahotan ya kara da cewa, mahaifin jariran baya nan lokacin da uwar jariran ta haihu, sai da hukuma ta kama Ma, sannan mahaifin ya gabatar da kansa. Ma, ta bayyana wa ’yan sanda cewa, bayan ta sayar da jariran ta raba kudin don biyan bashin banki da mahaifin jariran ya ci, yayin da sauran kudin ta yi amfani da su wajen sayen sabuwar wayar salula. Wu, ya kasance yana ci gaba da  biyan bashin kudaden cacar da yake yi.

Jami’an ’yan sandan sun yin kokarin karbo jariran daga Anhui tare da mika su ga iyayen Ma. A yanzu haka an tsare iyayen jariran don yanke musu hukunci inda suke jiran shiga gidan yari na wani lokaci. Bayan tsare mahaifiyar jariran da mahaifin tagwayen duk sun kashe kudaden da suka sayar da jariran.