Wata ta shekara 2 tana yi wa furanni roba ban-ruwa
Wata mata da ke birnin Kalifoniya a kasar Amurka ta yi suna a baya-bayan nan a kafar sada zumunta ta Facebook bayan da ta bayyana wani faifan bidiyo inda take nuna cewa ta gano furannin da take yi wa ban-ruwa tsawon shekaru biyu na roba ne. A ranar 28 ga Fabrairu ne matar mai suna […]
Wata mata da ke birnin Kalifoniya a kasar Amurka ta yi suna a baya-bayan nan a kafar sada zumunta ta Facebook bayan da ta bayyana wani faifan bidiyo inda take nuna cewa ta gano furannin da take yi wa ban-ruwa tsawon shekaru biyu na roba ne.
A ranar 28 ga Fabrairu ne matar mai suna Caelie Wilkies ta saki faifan bidiyon ga abokanta a shafinta na Facebook. Ta bayyana cewa, ta gano haka ne bayan da ta yi kokarin sauya wa furannin wuri. Sai tukunyar da ke dauke da furannin fashe yayin canja wurin inda ta gano cewa, an yi amfani da roba wajen like furannin.
Matar ta ce ta kwashe tsawon shekara biyu tana yi wa furannin ban-ruwa da ba su kula ta musamman kafin ta gano cewa, wahalar banza take yi.
Ta ce, “Na kasance tare da kyawawan furannin na tsawon shekara biyu. Ina alfahari da su. Suna da matukar kyau, launinsu mai kyau ne, suna da matukar burgewa.
“Na ajiye su a tagar dakin girki na. Ina da tukunyar ban-ruwa na musamman kuma ba na barin wani ya matso kusa da ita. Ina son furannin. A yau na yi niyyar sauya musu wuri. Na samo wa tukunyar kyakkyawan wuri da zan maida ta. Zuwa in cire ta ke da wuya na gano ashe furannin na bogi ne.
“Na kwallafa raina sosai a kan furannin nan. Nakan wanke ganyensu. Na yi kokarin sauya musu wuri inda za su fi jin dadi, amma kash na gano na roba ne!”
Faifan bidiyon da ta wallafa ya samu karbuwa sosai a makon nan ya kuma janyo hankalin mutane da yawa inda suka bayyana ra’ayoyinsu. Jaridun New York Post da Fod News ma sun ruwaito labarin.
A yayin da wadansu suke bayyana mamaki, wadansu sun bayyana irin yadda hakan ya faru da su a baya.
Daya daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu kan lamarin ta ce, “Ni ma na yi haka.” Ta kara da cewa, “Mahaifiyata ta sayo min irin wadannan furanni, bayan wani lokacin da na dube su sosai bayan shekara daya. A lokacin na fara tunanin me ya sa ba sa girma. A nan ne na sanya hannuna karkashin furannin, saboda in ji ko danye yake ko a bushe daga bisani na gano cewa bushashshen siminti ne.”