Wata uku uami’o’i ba su da wutar lantarki —SSANU
Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i ta Najeriya (SSANU) ta ce babu jami’a guda ɗaya mallakin gwamanti da ke iya biyan kuɗin wutar lantarkin da take sha
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa.
Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba na Naira dubu 70 da sauran sauye-sauye da ke tattare da shi zuwa ƙarshen watan Maris na shekarar nan ta 2025.
Shugaban Ƙungiyar SSANU ta Kasa, Kwamred ohammed Ibrahim, ne ya sanar da haka a yayin taron Majalisar Tuntuba ta Ƙasa (NAC) da ƙungiyar ta gudanar a Abuja.
Kwamred Ibrahim ya bayyana cewa har yanzu Gwamantin Tarayya da na wasu jihohi ba su fara biyan ma’aikatan jami’a sabon albashin ba, duk da kasancewarsu ƙwararru a fannoni daban-daban.
Game da zargin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa da neman xin hancin Naira miliyan takwas daga kowane shugaban jami’ar Gwamnatin Tarayya kafin su amince da kasafin kuɗin makarantarsa, ƙungiyar ta ce idan har hakan ta tabbata, to za su yaƙi lamarin kai da fata.
Ya ƙara da “idan ta tabbata, to wannan babban abin takaici ne, don a halin yanzu babu wata jami’ar gwamnati da ake da isassun kuɗaɗen biyan kuɗin lantarki.
“Daga cikinsu akwai waɗanda rabonsu da amfani da wutar an fi wata uku. Ta daga ina za su samu kudin da za su ba ’yan majalisar cin hanci Naira miliyan takwas-takwas.
“Idan har wakilan da jama’a suka zaɓa domin su tabbatar da cewa makarantun sun samun cikakkiyar kulawa babu tauyewa ne za su dawo suna neman cin hanci daga wurinsu, lallai za mu ɗauki mataki.
“Ina tabbatar maka cewa majalisa ba ta fi ƙarfinmu ba, za mu yaƙe su, domin a mazaɓunmu suke, za samu kayar da su,” in ji shugaban na ma’aikatan jami’a.