Wata uwa ta koma makarantar diyarta don samun ilimi

Wata uwa a birnin Sana’a, babban birnin kasar Yemen, wadda shekarunta sun fi 30, ta koma makaranta, inda ta shiga aji daya da ’yarta, kamar yadda jaridar Al Thawra ta ruwaito.Wannan uwa daliba, mai suna Aziza Muhammad Al Hanouma, ta shiga firamare ta Sam Bin Noah. Da jaridar Al Thawra ta tuntube ta kan dalilan […]

Wata uwa ta koma makarantar diyarta don samun ilimi
Wata uwa ta koma makarantar diyarta don samun ilimi

Wata uwa a birnin Sana’a, babban birnin kasar Yemen, wadda shekarunta sun fi 30, ta koma makaranta, inda ta shiga aji daya da ’yarta, kamar yadda jaridar Al Thawra ta ruwaito.
Wannan uwa daliba, mai suna Aziza Muhammad Al Hanouma, ta shiga firamare ta Sam Bin Noah. Da jaridar Al Thawra ta tuntube ta kan dalilan da suka sanya ta koma makaranta, sai Aziza Al Hanouma ta ce: “A lokacin da nike fama da jahilci, ina yawan jin kunya a duk sa’adda ’ya’yana suka bukaci in taimaka musu da aikin gida.”
Aziza Muhammad AlHanouma, uwa ce ga ’ya’ya biyar, wadanda ke karatu a makarantar Firamaren da take neman ilimi.
Kuma a cewar wannan uwa da ta koma mkaranta, a irin al’ummarmu mai ra’ayin rikau na tsofaffin al’adu, ’yan mata na barin makaranta a lokacin da suke kanana. Al Hanouma ta ce tana da wani hakki na mijinta da take son saukewa, tunda mijinta Ahmad likita ne a asibitin Al Thawra da ke babban birnin.
Ta ce, tana kokarin kammala Firamare, sannan ta shiga sakandare, har ta kai ga babbar kwaleji.
Shugabar makarant da AlHanouma ke karatu, ta ce ba ta taba ganin uwa da ke neman ilimi a makaranta daya da ’ya’yanta ba, a tsawon shekaru 23 da ta shafe tana aiki. Su ma ’ya’yan wannan uwa, sun ce karatun da mahaifiyarsu ke yi, yana kara musu kwarin gwiwa.
Kuma wannan mata mai neman ilimi, ta bayyana cewa, tana son a bayyana labarinta ne, domin ta karfafi gwiwar matan Yemen su bi sawunta. Alkaluman kididdiga sun bayyana cewa mata marasa ilimin zamani sun kai kimanin kashi 60 cikin 100 na matan kasar, a tsawon shekarun da suka gabata, musamman idan an yi la’akari da mazauna yankunan karkara.