Wata ’yar aiki ta caka wa wata wuka bisa zargin kwace mata saurayi
Wata ’yar aikin gida ta caka wa wata wuka da nufin yi mata kisan gilla saboda ta “kwace mata saurayi” kamar yadda kotu ta saurari karar. Yarinyar ’yar shekara 28, ’yar asalin kasar Nepal tana tsananin kishi da bakin cikin wata budurwa ’yar asalin Sri Lanka a kan saurayinta dan asalin Pakistan, don haka ta […]
Wata ’yar aikin gida ta caka wa wata wuka da nufin yi mata kisan gilla saboda ta “kwace mata saurayi” kamar yadda kotu ta saurari karar. Yarinyar ’yar shekara 28, ’yar asalin kasar Nepal tana tsananin kishi da bakin cikin wata budurwa ’yar asalin Sri Lanka a kan saurayinta dan asalin Pakistan, don haka ta yi yunkurin kasheta, kamar yadda yake kunshe a rahoton rahoton karar da aka gabatar.
A ranar 2 ga Afrilun bana, ’yar aiki ta hada kai da wata ’yar aiki da ta gudu daga gidan da take aiki, suka tarar wa wadda suke kishi a kanta, inda suka barbada mata yaji a fuska, bayan ta daina gani, sai suka sakata cikin na’urar hawa da sauka dogon gini (lifter), zuwa hawa na takwas. Da nufinsu su kasheta, don haka suka caka mata wuka a kai da kafada da ciki. Wadda aka caka wa wukar ta yunkura ta ture su, ta gudu, inda daga bisani ta samu aka kaita asibiti.
An kai rahoto ofishin ’yan sanda da ke Silicon Oasis a yankin Rashidiyya da ke Dubai ta kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Tuni ’yan sanda suka kama mai laifi, kuma ta amsa lafiinta.