Wata ’yar giya ta daba wa matar aure wuka
Ana tuhumar wata mata da ake zargin ’yar giya ce, mai shekara 33 da daba wa wata matar aure wuka a garin Osogbo na Jihar Osun, inda aka gurfanar da ita gaban kotun majistare. Matar mai suna Dayo Owolabi, an yi zargin cewa ta yi mankas da ruwan giya fiye da kima a ranar Lahadi […]
Ana tuhumar wata mata da ake zargin ’yar giya ce, mai shekara 33 da daba wa wata matar aure wuka a garin Osogbo na Jihar Osun, inda aka gurfanar da ita gaban kotun majistare.
Matar mai suna Dayo Owolabi, an yi zargin cewa ta yi mankas da ruwan giya fiye da kima a ranar Lahadi da ta gabata, inda wata rashin jituwa ta hada su da matar aure mai suna Latifa Kojo, inda al’amarin ya faru.
Wannan abin tsautsayi dai ya faru ne a Unguwar Arikalamu na garin Osogbo, inda gardama ta hada matan biyu suka cakume da fada, kuma daga bisani ’yar giyar ta yi amfani da wuka wajen raunata Latifa.
Tun farko, an kai rahoton al’amarin ga ofishin ’yan sanda na Dugbe, inda aka kama matar kuma aka gabatar da ita a kotu ranar Litinin da ta gabata. Sai dai ta bayyana wa kotun cewa ita fa ba ta aikata wannan laifi da ake tuhumarta da shi ba. Daga bisani lauyanta ya nemi kotu ta ba da ita a hannun beli.
Alkalin Kotun Majistare R.A. Olayemi ya amince a bayar da ita beli a kan Naira dubu 10 sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 4 ga Fabrairun nan.