Wata ‘yar Najeriya ta kashe kanta a Ghana

Wata ‘yar Najeriya dake zaune a kasar Ghana ta kashe kanta saboda rufe ma ta shaguna da hukumomin Ghana suka yi. Kungiyar ‘yan kasuwan Najeriya (NANT) reshen kasar Ghana ne suka sanar da rahoton a Abuja. Kungiyar ta bayyana hakan ne, yayin da kungiyar ta ziyarci mataimakiya ta musamman ga Shugaban kasa akan harkokin kasashen […]

Wata ‘yar Najeriya ta kashe kanta a Ghana

Wata ‘yar Najeriya dake zaune a kasar Ghana ta kashe kanta saboda rufe ma ta shaguna da hukumomin Ghana suka yi.

Kungiyar ‘yan kasuwan Najeriya (NANT) reshen kasar Ghana ne suka sanar da rahoton a Abuja.

Kungiyar ta bayyana hakan ne, yayin da kungiyar ta ziyarci mataimakiya ta musamman ga Shugaban kasa akan harkokin kasashen waje Misis Abike Dabiri-Erewa, inda suke bukatar hadin kan shugaba Muhammadu Buhari akan lamarin.

Shugaban kungiyar NANTS a Ghana Cif Chukwuemeka Nnaji, ya ce Misis Stella Ogonna Okpaleke, mahaifiyar yara uku ta kasha kanta a ranar 22 ga Satumba saboda rufe mata shugunan da aka yi.