Wata yarinya ta kubuta daga hannun matsafa a Legas

A makon da ya gabata ne al’ummar unguwar Ebute-Metta da ke Legas suka wayi gari da alhinin ɓatan wata yarinya mai suna Hauwa Umar, ’yar kimanin shekara 14 da haihuwa, bayan da wata maƙwabciyarsu ta aike ta wajen ƙawarta; inda a kan hanyarta ta dawowa gida ta haɗu da irin mutanen nan masu sace yara […]

Wata yarinya ta kubuta daga hannun matsafa a Legas

A makon da ya gabata ne al’ummar unguwar Ebute-Metta da ke Legas suka wayi gari da alhinin ɓatan wata yarinya mai suna Hauwa Umar, ’yar kimanin shekara 14 da haihuwa, bayan da wata maƙwabciyarsu ta aike ta wajen ƙawarta; inda a kan hanyarta ta dawowa gida ta haɗu da irin mutanen nan masu sace yara don yin tsafi da su, wanda ya sace ta, ya yi garkuwa da ita har na tsawon kwana biyu. 

Aminiya ta bi diddigin yadda lamarin ya faru, inda ta zanta da mahaifin yarinyar mai suna Malam Umaru, wanda ya shaida cewa da misalin ƙarfe 11 zuwa 12 na ranar Litinin ɗin ne matar da ta aiki yarinyar ta ba ta Naira 500 ta kai wani gida. Bayan da ta kai kuɗin, a kan hanyarta ta dawowa sai ta ci karo da wani matashi ɗan kimanin shekara 30 mai suna Damilare Adeboyin; wanda ya kira ta domin ta je wajensa. Da ya ga ta ƙi zuwa sai ya shammace ta, ya buga mata wani tsumma mai kama da hankici, inda nan take kuma ta fita daga hayyacinta. Sai ya dora ta a kan babur, ya tafi da ita. 

“A ranar ina gida amma matar da ta aike ta ba ta sanar mana ba. Da goshin Magariba na ga alamar yarinyar ba ta gidan sai na aika gidan da aka aike ta a dubo ko tana can tana wasa da yara, sai suka tabbatar mana cewa ai lokacin da aka aike ta da rana ta kai aike, ta koma gida. Nan fa muga shiga cigiyarta har sai da muka kwana muna nema har garin Allah ya waye; dare ya sake yi, kwana biyu muna nemanta ba mu gan ta ba a lokacin. Sai da garin Allah ya sake wayewa aka kira ni aka shaida mani cewa an ga ’yata tare da wani mutum yana tafe tana binsa a baya. Ko da muka je an miƙa lamarin ga hukumar ’yan sanda, sai muka garzaya zuwa ofishinsu,” inji shi.

Malam Umar ya ƙara da cewa a lokacin da aka gano yarinyar, ba ta iya magana kuma jikinta babu babu ƙarfi ko kaɗan a tare da ita, domin ko hannunta ba ta iya ɗagawa. 

“Nan muka kai ta babban asibitin Legas, muka biya Naira dubu hudu a banki, inda jami’an asibitin suka tabbatar mana cewa ba a yi lalata da ita ba, wanda haka ke nuna cewa ya sace ta ne da nufin yin tsafi da ita kawai. Daga nan muka dawo da ita gida muka yi ta yi mata taimako da addu’a da ake karanta mata a kunnuwanta da kuma rubuntun sha. Da haka ne har Allah Ya taimake mu bakinta ya buɗe, bayan kwana 6 da gano ta, domin a sa’ilin da muka gano ta, hankalinta ba ya jikinta, ta juye tamkar mara hankali. Ba ta iya Magana, ba ta iya gane komai amma alhamdu lillahi, da taimakon Allah addu’ar da aka yi ta yi yanzu ta dawo ga hayyacinta,” inji shi. 

Aminiya ta zanta da yarinyar mai suna Hauwa, wacce ga duk alamu ta sami sauƙi sosai ta kuma amsa duk tambayoyin da wakilin Aminiya ya yi mata. Ta ce bayan mutumin ya kira ta ta ƙi zuwa sai ya shammace ta ya shaƙe mata wuya. “Ba zan iya gane kalar kyallan da ya shafa mani a fuska ba, domin sai da ya shaƙe mani wuya, hankalina ya gushe, ban san yadda na hau babur ɗinsa ba. Da muka isa gidan da ya kai ni, na tarar da yara uku an ɗaure su da jan tsunmma. Ni ma haka aka yi mani, ya kawo mani abinci wanda ban iya gane kalarsa ba. Sai na ƙi karɓa, bayan wani lokaci wani mutum ya zo ya fita da yaran su 3 daga ɗakin da muke. Daga nan bayan an jima kaɗan sai na ga an jefo gangar jikinsu babu kai,” inji ta.

Ta ce lokacin da aka fita da yaran 3, shi wanda ya ɗauko ta yana tare da ita. “An ce an kama shi ne yana tafe ina bin sa, ni a wannan lokacin ban san inda kaina yake ba, domin ko da aka kai ni gida ban gane gidanmu ba, sai da mahaifiyata ta shafa mani man Robb mai zafin nan, sannan idona ya buɗe, na fara gane gida,” inji ta.

Kamar yadda mahaifin yarinyar ya shaida, ’yan unguwarsu sun tabbatar da cewa, wanda ake zargin ya sace ta, Damilare Adeboyin ɗan daudu ne, kana ɗan ɗuwaɗi ne. Ya ce ’yan sandan da ke binciken lamarin sun tabbatar da haka, bayan da suka binciki wayar salularsa. Jami’an ’yan sandan sun je cocin da wanda ake zargin yake bauta domin zurfafa bincike, inda limamin cocin ya je ofishin ’yan sandan ya shaida masu cewa cocinsu bai da masaniya bisa mummunar ɗabi’ar da aka kame wanda ake zargin da shi.

Sarkin Zabarmawan unguwar Ebute-Metta, Alhaji Garba Kwaini, shi ne wanda ya sanar wa jami’an ’yan sandan da suka kame wanda ake zargin. Ya shaida wa Aminiya cewa za su yi iya ƙoƙarinsu don ganin an hukunta wanda ake zargin tare da bi wa yarinyar haƙƙinta. Ya ce duk da dai iyayen yarinyar talakawa ne, za su yi iya ƙoƙarinsu don ganin an ladabtar da wanda ake zargin gwargwadon laifin da ya aikata.

A nasa ɓangaren Kwamred Sakaba, shugaban kungiyar Matasan Arewa a jihohin Kudu (NNYO), ya ce suna ta kokarin ganin an hukunta wanda ake zargin. Ya yi kira ga iyayen yara da su ƙara sanya ido a kan ’ya’yansu, la’akari da yadda masifar masu satar yara domin yin tsafi da su ke ƙara yawaia. Haka kuma ya yi kira ga hukuma da ta tabbatar ana yi wa waɗanda aka samu da irin wannan laifi hukuncin da ya dace da su, don haka ya zama izna ga na gaba.