Watakila Adebayor ya koma West Ham United

Jaridar Mirror ta kalato cewa akwai yiwuwar kulob din West Ham United na Ingila ya dauke dan kwallon kulob din Tottenham da ke Ingila haifaffen Togo Emmanuel Adebayor kafin a rufe kasuwar saye da kuma sayar da ’yan kwallo.  Sai dai rahoton ya nuna akwai yiwuwar zai koma kulob din ne a matsayin na aro.  […]

Watakila Adebayor ya koma West Ham United
Watakila Adebayor ya koma West Ham United

Jaridar Mirror ta kalato cewa akwai yiwuwar kulob din West Ham United na Ingila ya dauke dan kwallon kulob din Tottenham da ke Ingila haifaffen Togo Emmanuel Adebayor kafin a rufe kasuwar saye da kuma sayar da ’yan kwallo.  
Sai dai rahoton ya nuna akwai yiwuwar zai koma kulob din ne a matsayin na aro.  Rahoton ya ce kulob din yana tunanin aika shi kulob din West Ham ne don ya samu saukin albashin Fam dubu 100 da yake biyansa a duk mako alhali ba kasafai yake yi wa kulob din kwallo ba, don ya rage asara.
Adebayor dai ya dade a kulob din Tottenham kuma ya yi wa kulob da dama kwallo a matsayin na aro ciki har da kulob din Real Madrid na Sifen.