Watakila ba zan mutu ba – Indiya mai shekara 179

Wani tsoho wanda sana’arsa a da ita ce gyaran takalmi a Arewacin Indiya mai suna Mahasta Murasi ya ce an haife shi a watan Janairu na shekarar 1835, wanda hakan ya sa a yanzu yake da kimanin shekara 179 a duniya. A wani rahoton kididdiga na kasar Indiya, an gano cewa an haifa mutumin ne […]

Watakila ba zan mutu ba – Indiya mai shekara 179

Wani tsoho wanda sana’arsa a da ita ce gyaran takalmi a Arewacin Indiya mai suna Mahasta Murasi ya ce an haife shi a watan Janairu na shekarar 1835, wanda hakan ya sa a yanzu yake da kimanin shekara 179 a duniya.

A wani rahoton kididdiga na kasar Indiya, an gano cewa an haifa mutumin ne a birnin Bangalore a ranar 6 da watan na Janairu na shekarar 1835 kamar yadda ya fada, sannan kuma ya yi rayuwa a garin baranasi tun shekarar 1903.

Haka nan kuma rahotannin sun nuna cewa Mahashta ya kasance yana sana’ar gyaran takalmi ne a garin na baranasi na tsawon lokaci har zuwa shekarar 1957, lokacin da aka ruwaito ya daina aiki a lokacin yana da shekara 122 saboda tsufa da rashin cikakkiyar lafiya. 

“Na rayu na tsawon lokaci, wanda har tattaba kunne na sun rasu sun bar ni shekaru da yawa da suka wuce,” inji Mista Murasi.

“Kamar mutuwa ta manta da ni ne. ka duba rahoton kididdiga na mutanen da suka mutu a baya. Ba a taba samun wanda ya wuce shekara 150 ba ko kuma har ya wuce shekara 170 kafin ya mutu ba. Tun lokacin da na ga haka, sai nake tunanin ko ba zan mutu ba. Abin dai akwai daura kai. Amma zan ci gaba da rayuwata kawai.”

Takardun shaidar haihuwar mutumin da katin aiki da sauran takardunsa suna tabbatar da abin da ya fada a game da shekarunsa, amma sai dai ba a gudanar da wani gwaji ban a asibiti da zai tabbatar da hakan.

Rahoton ya kuma nuna cewa likitan da Murasi ya ziyarta na karshe ya mutu tun a shekarar 1971, don haka babu cikakken bayani a game da lafiyarsa da kuma yanayin jikinsa.