…Watakila Daniel Amokachi ko Baba Ganaru su zama kocin Kano Pillars

Tsohon Mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Daniel Amokachi da kuma kocin kulob din Nasarawa United Mohammed Baba Ganaru suna daga cikin kococin da suka fara yunkurin zama kocin kulob din Kano Pillars kamar yadda rahotannin da ke fitowa suka nuna.A ranar Litinin da ta wuce ne dai Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi […]

…Watakila Daniel Amokachi ko Baba Ganaru su zama kocin Kano Pillars
…Watakila Daniel Amokachi ko Baba Ganaru su zama kocin Kano Pillars

Tsohon Mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Daniel Amokachi da kuma kocin kulob din Nasarawa United Mohammed Baba Ganaru suna daga cikin kococin da suka fara yunkurin zama kocin kulob din Kano Pillars kamar yadda rahotannin da ke fitowa suka nuna.
A ranar Litinin da ta wuce ne dai Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da korar kocin Kano Pillars Okey Emordi saboda rashin kokari a kakar wasa ta bana.  Daga nan ne gwamnan ya amince da rusa shugabannin gudanarwar kulob din inda tuni ya maye gurbinsu da wasu sababbi a karkashin shugabancin Kabiru Baita.
Shi dai Amokachi, an kore shi ne a matsayin mataimakin koci a lokacin da Stephen Keshi yake jagorantar kungiyar kuma tun bayan korarsa kungiyoyin kwallon kafa da dama a Najeriya suka rika rububinsa.  Ya taba hortrwa a kulob din Nasarawa United da kuma Enyimba da ke Aba.
Shi kuma kocin Nasarawa United Mohammed Baba Ganaru shi ma ya nuna sha’awarsa wajen horar da kungiyar Kano Pillarsa.
A ranar Talatar da ta wuce ne kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa na zakulo sabon kocin ya fara aikinsa, kuma ana sa ran nan da lokaci kankane zai gabatar da sabon kocin don ganin ya fara aiki.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram