Watakila Enyimba ta zama zakara a jibi
A cigaba da gudanar da gasar rukuni-rukuni ta Najeriya da aka fi sani da GLO Premier League a jibi Lahadi ne ake sa ran kulob din Enyimba da ke Aba zai zama zakara a wasa karo na 37 da kulob din zai yi da na Warri Wolbes. A halin yanzu Enyimba ce take saman teburin […]
A cigaba da gudanar da gasar rukuni-rukuni ta Najeriya da aka fi sani da GLO Premier League a jibi Lahadi ne ake sa ran kulob din Enyimba da ke Aba zai zama zakara a wasa karo na 37 da kulob din zai yi da na Warri Wolbes.
A halin yanzu Enyimba ce take saman teburin gasar da maki 68 daga wasanni 36 sai mai biye da itaWarri Wolbes mai maki 62 daga wasanni 36, sai Wikki Tourist da ke Bauchi ta uku da maki 60 yayin da Giwa FC na Jos ita ma mai maki 60 a matsayin ta hudu.
Idan Emyimba ta samu nasara a wasanta da Warrri Wolbes ko ta yi kunnen doki, babu makawa ita ce za ta kasance zakara a gasar rukunin firimiya ta Najeriya a bana. Amma idan Warri Wolbes ta doke ta a wasan to sai Enyimba ta jira makon gobe lokacin da za a yi wasan karshe a gasar kafin ta san matsayinta. Enyimba za ta yi wasan karshe ne a makon gobe da kulob din Sunshine Stars na Akure da ke matsayi na uku.
Kulob din Enyimba dai ya taba lashe gasar rukunin firimiya na Najeriya har sau shida. Ya lashe a shekarar 2001 da 2002 da 2003 da 2005 da 2007 da kuma a 2010. Sai kuma a bana da take sa ran lashe na bakwai.