Watan Babbar Sallah ya bayyana a Saudiyya
Za a yi Idin Babbar Sallah ranar Lahadi 16 ga watan na Yuni.

Muslim pilgrims gather around the Kaaba, Islam’s holiest shrine, as they perform Eid Al-Adha morning prayers in Mecca, on June 28, 2023. (Photo by Abdulghani BASHEER / AFP)
Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Zhul Hijjah a yammacin wannan Alhamis dis.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa shafin Haramain ya wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa gobe Juma’a ne ɗaya ga watan na Babbar Sallah.
- Kotu ta sa ranar bayyana huruminta kan rushe masarautun Kano
- An kama maniyyatan Hajji da hodar iblis a Legas
Hukumomin na Saudiyya sun kuma ce ranar Asabar 15 ga watan Yuni ne za a yi tsayuwar Arafa, yayin da za a yi Idin Babbar Sallah ranar Lahadi 16 ga watan na Yuni.
Tuni dai miliyoyin maniyyata ke ci gaba da isa Saudiyya a ƙoƙarinsu na aiwatar da ibadar aikin Haji.
Kawo yanzu maniyyatan fiye da miliyan daya sun isa kasa mai tsarki a shirye-shiryen sauke farali a bana.