Watsattsaken wasikar waskiya (I)

Watsattsaken wasikar waskiya Walwalin waliyon walkiya Wautar watangaririya Wawurar wariya Wafce-wafcen wukiya   Baban-gargada Burga da baragada Baban bugun gada Baturen Bagauda Bargar dawaki da danda   babatu da buruntu Surutun mai tagiya da tuntu barambarama rututu Da manufar kulla kutu-kutu Wai suna bayar da sautu   Miyagu na ta sambatu An fasko masu shigar […]

Watsattsaken wasikar waskiya (I)

Watsattsaken wasikar waskiya

Walwalin waliyon walkiya

Wautar watangaririya

Wawurar wariya

Wafce-wafcen wukiya

 

Baban-gargada

Burga da baragada

Baban bugun gada

Baturen Bagauda

Bargar dawaki da danda

 

babatu da buruntu

Surutun mai tagiya da tuntu

barambarama rututu

Da manufar kulla kutu-kutu

Wai suna bayar da sautu

 

Miyagu na ta sambatu

An fasko masu shigar burtu

Karatunsu har da Satu

Su dai sun yi batu

Hassada ta sa sun zautu

 

kwanji

Da karaji

Rashin ji

Laluben kunji-kunji

bulluko wa kasa kurji

 

Kankamba da kwaramniya

Kata-katar kiriniya

kumbiya-kumbiya

Tsallen jaba da gafiya

Kusu mai kurmusun tsiya

 

Tuhumar karya

kwarya dai ta bi kwarya

 

Manya na dirkaniya

Hassada da butulcin tsiwa

Suna ta yi wa al’ummma tsuwwa

Tufka da warwarar waskiya

Sai a fasko mutan Haurobiya

 

Maiduka yai mana kariya

Mu kiyayi masu kwakwazo a rariya

Mu zamto masu juriya

Yarima da Gimbiya

Lumana ta fi mulkin duniya

 

Sara da daukar dawainiya

Hana zaluncin ’yan danniya

Masu dabi’ar hawainiya

Da ke sauya salon zamiya

Zaburar dokin zuciya

 

Baba kyale ’yan jagaliya

Masu jagwalgwalon jan tsiya

Da jangalewar jayayya

Juwa-juwar hajijiya

Tsaya Baban-burrin-huriyya

 

Tsirin tsiyakun tsinannu

Masu tauye mudu da hannu

Sun yi dako a tsamiyar tsinannu

Fuskarsu murtuke sun sha kunu

Matafiyansu da zaunannu

 

Baba-Ojo mai gonakin Ottawa

Tsohon nan ya yi yawa

Zagon kasa yai wa ’Yar’bishiya

Tadiye kafar Haurrobiya

Yanzu yana yi wa Baba adawa

 

Wai shi ga kartagi uban ’yan caca

Al’umma tai masa ca

Tsoho mai Iburo da acca

Masu mulki yai musu faca-faca

Shi ma za ai masa kaca-kaca

 

Shi ne uban carafke

Mai canke-canke

Ba wani mugu sai shi

Ba ya so a caccake shi

An fasko wanga take-take

 

Baba-Ojo

Gwanin gwanjo

Dukiyar al’umma ya wawushe

Ya bar mu muna ashe- a she

Shi kuwa yana ta rawar banjo

 

Mutumin da debi dukiya yai fatali

Ya ce babu wanda ya iya tattali

Sai shi da ya iya gantali

Da jajibe-jajiben rashin hankali

Shi ya fara rusa wa kasa tubali

 

Wanzami ba ya son jarfa

Sai a ba shi tuffa

Garinsa ya samu nonon tarfa

Sai ya ji dadin kwafa

Ya toshe mana kowace kofa

 

An hango shi ta kowace kafa

Yana makircin tsirfa

Wai ka da a ce ya tsufa

Ko’ina sai ya dauki kafa

Wai don a ce masa kakarfa

 

Lamarin tsoho ya zurfafa

Muguwar manufarsa ta zafafa

Magabta  na binsa sau da kafa

Ko ya shuka samfarera su dafa

Fandararsu ta sa sun yi zufa

 

 

Mai lambu

Yai limbu-limbu

Wai ya nada kambu

Zai dundume kururu da dambu

Baba za a garkame wa gambu

 

Masu lebba subu-subu

Kun yi gini da yunbu

Sannu taron tababbu

Jibar jibga rabu

kuri’ar zumbutun zababbu

 

Kwashe kudi dungurungum

A duhun dundumdurundum

Ana ta durundum

Wasan madundumu dududum

Ya ki jan bakinsa yai gum

 

Ku sha kuruminku kurum

Masu cin tumu tutum

Kidan gurminsu gurungurum

Na dakama dankam yai dulkum

Mu dai mu yi bakam

 

Mun huta da kwamarto

Don kurciya na ta koto

Jirkicewar mai dan boto

Baba-ojo ya ba ku toto

Baban gada-gada ya wafto

 

Haurobiyawa a halarto

Kowa ya karanto

Kura ce aka kwanto

bauna ma tai kwanto

Baba ban da ambato