Watsi Da Harshen Hausa: Har yanzu a cikin bauta muke – Sarkin Katsina

Mai mairtaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bayyana cewa har yanzu al’ummar Najeriya na cikin kangin bauta, musamman saboda yadda aka yi watsi da harshen Hausa da sauran harsunan gida wajen gudanar da al’amuran yau da kullum da ma harkokin gwamnati. Sarkin wanda ya bayyana haka a fadarsa a makon jiya, a lokacin […]

Watsi Da Harshen Hausa: Har yanzu a cikin bauta muke – Sarkin Katsina

Mai mairtaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya bayyana cewa har yanzu al’ummar Najeriya na cikin kangin bauta, musamman saboda yadda aka yi watsi da harshen Hausa da sauran harsunan gida wajen gudanar da al’amuran yau da kullum da ma harkokin gwamnati.

Sarkin wanda ya bayyana haka a fadarsa a makon jiya, a lokacin da tawagar kungiyar Marubuta ta kasa (ANA) ta kai masa ziyarar girmamawa, ya ce al’amuran kasar nan sun lalace ne saboda watsi da aka yi da harshen Hausa, aka rungumi harshen Turanci wajen tafiyar da al’amuran gwamnati da na ilimi.

“Na samu rahoton da ke cewa a makarantunmu na firamare, an daina koya darussan Hausa da addinin Musulunci. Yau nake shirin rubuta korafi kan al’amarin sai kuma ga shi kun zo. Don haka ku karfafa harshen Hausa, a kafa shi yadda ‘ya’yanmu za su tashi da Hausa, su koyi Hausa, ba wai kawai ku rika shirya taro a yi jawabai, a yi tafi a tashi ba.  Idan ka je Saudi Arebiya, da Larabci suke komai, idan ka je Jamus da Jamusanci suke gudanar da harkokinsu, amma mu nan sai dai cikin Ingilishi. Shi ya sa nan muke ta fama, a ce wai dalibi sai ka ci Ingilishi da lissafi. Wannan ya nuna har yanzu muna cikin kangin bauta,” inji sarkin.

Ya bayyana cewa akwai bukatar al’umma su kasance masu daraja harshensu da al’adunsu, domin da su ne ake ci gaba. “Kuma duk Afrika ta Yamma ko ma mu ce Afrika gaba daya, babu yaren da ya yi zurfi da amsuwa a duniya irin Hausa, amma ana neman tura shi baya. Idan dai aka ci gaba da haka, nan gaba za a nemi yaranmu su kasa kawo bayani cikin Hausa. Na taba tambayar wasu yara mene ne ma’anar dogon hannu? Idan aka ce mutum yana da dogon hannu, me ake nufi? Suka kasa kawo ma’anar. Na ce masu idan an ce mutum na da dogon hannu, ana nufin mutum barawo ne ke nan.”

Sarkin na Katsina ya nemi marubuta da su maida hankali wajen yin rubuce-rubuce masu inganci cikin harsunan gida, yadda za su rika koya tarbiyya da fadakar da al’umma. Kamar yadda ya ce: “Yanzu littattafai masu azanci irin su Magana Jari Ce da Ruwan Bagaja da Gandoki da sauransu, sun fara bacewa. Sai ka ga matasanmu wai su ’yan birni, suna yin shiga irin ta Turawa da sauransu. Harshenmu, suturunmu abubuwa ne masu kyau, amma duk mun watsar. Ko Ingila ka je, idan ka sanya suturunka na gargajiya, kai za a kalla kuma a ba ka muhimmanci fiye da wanda ya sanya kwat da zanzaro, domin naka ya fi muhimmanci da kima.” 

Ya kara jaddada cewa, irin yadda aka banzatar da harshen Hausa wajen koyarwa, shi ya sanya aka samu ci baya wajen kere-kere da kimiyya. “Yaren nan namu da muke rainawa, shi ne karfinmu, shi ne ci gabanamu. Yau da ake maganar cewa kasar China ta ci gaba, da yarensu na Sinanci suke koyarwa, suke yin darussan kimiyya da fasaha da injiniyanci, shi ya sanya suka ci gaba.”

Ya kuma koka da sabon tsarin ilimi, inda aka soke koyar da daliban makarantun firamare darussan harshen Hausa da kuma addinin Musulunci. “Maganar dakatar da koyar da daliban firamare Hausa da addinin Musulunci, ni dai zan rubuta korafi domin gwamnati ta duba. Ku kuma a matsayinku na marubuta, ya dace ku yi rubuce-rubuce, ku tallafa domin al’amarin ya yi karfi ya samu amsuwa. Ya zama dole mu rika yin magana kan abin da zai amfane mu. Yanzu ina jaridun Gaskiya Ta Fi Kwabo kuma ina New Nigeria? Duk an kashe su, kuma mun yi shiru mun ki magana. Ni dai zan ci gaba da magana, duk abin da zai cuci talakawana, zan yi magana. Ya rage ruwan mai magana ya je ya fadi abin da yake so, amma ni sai na kare talakawana.

“Ku ya kamata ku yi kwamiti, ku sanar da Gwamnatin Tarayya, jihohi da kananan hukumomi, ga matsalar da ake ciki, ga shawararku, mu kuma sai mu mara maku baya. Haka ake yi. Ni dai zan rubuta korafi ga gwamnati sai an dawo da koyar da wadannan darussa na Hausa da kuma addinin Musulunci. Kuma kuna ganin Hausar nan kamar wata abar wulakantawa. Ku sani cewa fa ana nazarinta har Jami’a, akwai Farfesa-farfesa da yawa na Hausa. Kai ne kake ganinta kamar wani karamin abu, a lokacin da aka ba ka takarda ka yi rubutu da Hausa, sai ka ga kana kame-kame,” inji Sarkin Katsina.

Ya yaba da marubutan da suka kai masa ziyara, sannan ya ba su shawara da cewa: “Wannan taron naku kun yi kokari saboda kun jawo hankalin jama’a amma dai bai isa ba, sai kun jajirce kun ci gaba da magana tare da aiki tukuru wajen fadakarwa da jawo ra’ayin al’umma su fahimta da muhimmancin al’adunsu, yarensu da sauransu. To yanzu idan aka ce an hana koya wa yaranmu yarenmu da addininmu, to me ya rage kuma? Me ake tunanin za su kasance nan gaba?”

Haka kuma ya koka da yadda aka wayi gari aka kashe Kwalejojin Ilimi, wanda ya ce bai dace ba, domin an durkusar da ilimi. “Kai da za ka koya wa yara ilimi, kuma ba a koya maka kimiyyar koyarwa ba, to ta yaya za ka koyar? Mu tuna da cewa yara fa kamar dabbobi suke, ba su san komai ba. To ta yaya za ka koyar da dabba wani abu alhali ba ka san hikimomi da dubarar koyarwa ba?

“Mu nan, mu muka raina kanmu, domin mun watsar da duk abi abu mai kima da muka mallaka, muka bari komai ya lalace. Lallai ya dace mu farka daga barcin da muke, mu gyara. Ni dai kam ba zan bari amanar da aka dora mani ba ta salwanta. Dama haka abin yake a shari’ance, idan kana iya bugawa ka buga, idan magana ka iya ka yi magana, idan kuma ba ka iyawa ka kyamaci abin a zuci. to ni ban zo nan wajen gazawar ba.”

Daga karshe, Sarki ya yi addu’a ga marubutan da suka kai masa ziyarar girmamawa. “Ina yi maku addu’a, Allah Ya dora mu kan daidai, mu aikata daidai kuma mu ga daidai a rayuwarmu. Allah mu ke yin kuskure, Kai ba ka kuskure, kullum sai mun sabe Ka, Ka yafe mana, Ka ba mu lafiya da zama lafiya. Idan lokacinmu ya zo, Ka ba mu ikon cikawa da imani.”