Watsi da mara lafiya: Kungiyar Likitoci ta fusata kan dakatar da likita a Kano

kungiyar NMA ta ce kamata ya yi a mayar da hankali wajen kula da halin da fannin lafiyar ke ciki da inganta hakkokin ma’aikatan bangaren

Watsi da mara lafiya: Kungiyar Likitoci ta fusata kan dakatar da likita a Kano

Wani asibitoci a Najeriya

Kungiyar Likitoci ta Kasa (NMA) reshen Jihar Kano ta bayyana rashin jin ɗacinta game da dakatarwar da Hukumar Kula da Asibiticin jihar Kano ta yi wa wata likita a Asibitin Kwararru na Muhammad Abdullahi Wase.

A cikin wata takardar mai dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar, Dokta Abdullahi Kabir Sulaiman da sakatatenta, Dokta Abdurrahman Ali, ta ce dakatarwar da aka yi wa likitan ba ya bisa ka’ida.

Sanarwar ta ci gaba da cewa kamata ya yi a mayar da hankali wajen kula da halin da fannin lafiyar ke ciki ta yadda aka yi wasarere da hakkin ma’aikatan lafiya da rashin kayan aiki da sauran abubuwa masu kama da haka.

Kungiyar ta bayyana cewa ma’aikatan lafiya suna fuskantar cin zarafi da rashin tsaro daga marasa lafiya da ’yan uwansu, lamarin da yake zama illa ga kwazon ma’aikatan wajen gudanar da ayyukansu.

A cewar takardar, irin wannan cin zarafi ne ya sa kungiyar ta dauki matakin shari’a akan mutanen da suka kai wa membobinta hari a yayin da suke bakin aiki.

A karshe sanarwar ta ja hankalin Hukumar da ta mayar da hankali wajen yin abin da ya dace a harkar lafiya da kuma masu kula da marasa lafiyar.

Kungiyar ta nemi Gwamnatin Jihar Kano da ta kara albashi da alawus na ma’aikatan lafiya don kara musu kwarin gwiwar aiki.

Idan za a iya tunawa a makon jiya ne Hukumar ta bayar da sanarwar dakatar da wata likita bisa zargin ta da yin ko-in-kila- ga wani maras lafiya.

A yayin da yake bayar da sanarwar, shugaban hukumar, Dokta Mansur Nagoda ya bayyana cewa Hukumar karkashin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba za ta lamunci yin wasarere da aiki daga jami’anta ba, don haka a cewarsa ta dauki wannan mataki a kan likitar nan take don ya zama izna ga na baya.