Wawar wadakar wauta
Belin-auta Billen-wauta Balbbalin wuta Beli-belin kubuta bali-balin kirjin zarata Gwamna gwarangwam Gwangwam Gwangwanin gudunmuwa Gararumar ’ya’yan mowa Gurmin gurungurum Gudumar gunkin gumaka Garnakakin cinnaka Gardin garada ga naka Guntun tumun kaka Gangaren gamsakuka Talalar talaucin ’ya’yan bora Ana ta kwada mana gora Shin daga ina za mu dora Almajirai na ta bara […]
Belin-auta
Billen-wauta
Balbbalin wuta
Beli-belin kubuta
bali-balin kirjin zarata
Gwamna gwarangwam
Gwangwam
Gwangwanin gudunmuwa
Gararumar ’ya’yan mowa
Gurmin gurungurum
Gudumar gunkin gumaka
Garnakakin cinnaka
Gardin garada ga naka
Guntun tumun kaka
Gangaren gamsakuka
Talalar talaucin ’ya’yan bora
Ana ta kwada mana gora
Shin daga ina za mu dora
Almajirai na ta bara
Mahandaman lalita na ta dara
Mun yi dako muna jira
Za ku zo kuna kira
Mu ce sannnunku abokan hira
Ku ci gaba da gantsara
Zabi-sonka ba ya faskara
An tsuwurwurta ta’adi
Maimakon tsimi da tanadi
Ga lakume kudin lukudi
Santsi na dauka da cikar wa’adi
Sakamakon aiki ne madadi
Baban-burin-huriyya
Makudai sun zurare a rariya
Ana nai maka kiren karya
Tsimin tsamiya
Tsarin zamiya
Wasu sun fake da batun laulayi
Baba ka yi jinya mai tsayi
Sun samu sake
Matsabbai duk sun mutsutttsuke
Za su maisshee da talakawa bayi
Baba ka taka musu burki
Cikinsu akwai mutanen kirki
Miyagu sai sun sha dukan maburki
Miyarmu ta yi burkaki
Har mun fara cin buski
An ce ka yabi Gandun aiki
Na birnin dabo ya biya ladar aiki
Gwamnanmu Mai samari
Ayyyukansa sun bayyyana a sarari
Gwamnan dakin-kara mutumin kirki
Bini-ina-wai
Talakawa na wai wai!
Kun ki ba da kudin kawai
Dundumin dawan dawai
Bnambamin buwai
dimbin alfanun damina
Hatsi ya zo an amfana
Sai mu hada da kiwon jimina
Farfesu na sa a fyace majina
Marasa galihu na neman majingina
A raya birane da karkara
’Yan takara
Ku daina taka kara
Ko ku debi kudinmu ku yi kakara
A daina haifar mana da asara
Ai tattali
A gyara muhalli
Ban da aikin rashin hankali
Mahaya ingarman karafa mu yi tozali
dabi’arku babu cin zali
Baba ka zare kansakali
Tsininta yana walwali
Ka dumfari masu jefa mana zullumi
Ko masu fashi da mukami
Ka tabbatar an yi musu solsali
Tun sa’addda Baban-burin-huriyya ya dare bias karaga cikin shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje yake ta fafatawa da SAMARIN KUSU da‘’YAN MATAN JAbA DA GAFIYA, wadanda suka bula mana lalita, suka haiar wwa tattalin arzikin Haurobiya ya koma tata, har aka zo ana kata-kata. Cikin sa’a da hukuncin Mai-duka sai Baba ya jinka wa Iro Mugun madambaci samandagarin samarin kusu, har aka samu aka cafko wadanda suka karbi rabonsu daga hannun SAMUN-BOM-DA-SAUkI ga mace-da-dazane HAR YANZU ANA TA FAFATAWA. Uwa-uba dan kullin damin matsabban da baba ya jinka wa gungun gwamnonin kasar nan don ssu ceto al’umma daga hannun dAN AUTAN TALAUCI sai wasu ssuka karkatar da akalarsa. Wannnan lamari dai babu dadiin ji!
Batu na ingarman karfen karafa, mun gaji da yi muku kashedi, nan gaba kowa ya yi da kyau zai ga da kyau. Lallai wajibi ne ku koyi TSARIN TSIMI DA TANADI, musamman dabarar nan ta FIFITA MUHIMMANCIN BUkATUN AL’UMMAR da kuke jan ragamarta.
Ayyukan raya kasa na da muhimmmanci, amma akwai lokutan da LADAR kWADAGO ta fi alfanu, DOMIN Malam mai yaren Hau-hau wajen hawan sa ba tare da sa-in-sa- ba ya ce DA RUWAN TUMBI AKE JANYO NA KWAKWARE.
Mun yi fama da SUNkURUN SARAF-NA-SAdAF a karkashin jan ragamar JAM’IYYA MAI dAN BOTTO DA SANDA JIRGE, wadda ta shafe shekara sili da manuniyar sama tana Jirga Haurobiyawa, har Mai-duka ya bai wa TSINTSIYA karfin SHARA ta share mana su. Masu hankali a kwanyarsu kada mu bari a koma gidan jiya, musamman tun da Baba ya gama jinya ba za mu yarda miyagu su ci gaba da yi masa jayayya ba.
Wannan al’amari da gwamnoninmu suka tsuwurwurta ai BATU NE NA BILLEN WAUTA DA WADAkAR WAKA-CI-KA-TASHI!
Ganin wannan TA’ASA da aka tafka akwanon TASA, har ta kai ga ana ta SA-IN-SA tsakanin Baban-burin-huriyya da gungun gwamnoni, ina ganin akwai bukatar mu tagaza wajen nusar da masu mulkin al’umma muhimman bukatun kyautata rayuwa da ya kamata a ce sun tunkara, don kada su karar mana da dukiyar kasa a wajen holewa da SHARHOLIYA.
Haurobiyawa mu hada karfi da karfen karafa, ta yadda z amu fice daga DUMA, mu hana masu mulki karkewa da DAMA-DAMA,har su DAMALMALA al’amura a zo ana LALA!