Wayar Blackberry ta koma gidan jiya

Kamfanin wayar Blackeberry ya kirkiro wata sabuwar waya ta komai da ruwanka ta daban, mai inkiyar Classic kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.Wayar tana da madannin lambobi da harufa wato (Keyboard) irin na wayoyin kamfanin na da, da ya sa ta yi fice kafin wayoyin wasu kamfanonin su sha gabanta a farin […]

Wayar Blackberry ta koma gidan jiya
Wayar Blackberry ta koma gidan jiya

Kamfanin wayar Blackeberry ya kirkiro wata sabuwar waya ta komai da ruwanka ta daban, mai inkiyar Classic kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Wayar tana da madannin lambobi da harufa wato (Keyboard) irin na wayoyin kamfanin na da, da ya sa ta yi fice kafin wayoyin wasu kamfanonin su sha gabanta a farin jini.
Bayan madannin na zahiri, wayar Classic din tana kuma da madanni irin na wayoyin zamani da ke kan fuska wayar wato  (Touchscreen). Haka kuma tana da kyamara a baya mai karfin megapidel takwas, ga hanzarin kama intanet kamar yadda kamfanin ya bayyana.
Masu lura da dabarun kasuwanci sun ce kamfanin ya koma tsarinsa ne na da, domin ya farfado da kasuwarsa.Kuma wasunsu na ganin da wuya hakan ya jawo hankalin wasu mutanen, kodake dai zai iya sa kasuwar wayar ta dore.
Wata mai lura da harkokin kasuwanci, Carolina Milanesi, na ganin wannan dabara ce ta rike mutanen da suke amfani da wayar kamfanin maimakon neman karin wasu sababbi. Ta kara da cewa tana ganin watakila mutanen da suka saba da wayoyi na zamani masu madanni na cikin fuska (Touchscreen) su ga Classic din a matsayin wani abin burgewa, su karbe ta, saboda madanninta na zahiri.