Wayar lantarki ta halaka dan agaji

Wayar wutar lantarki ta yi sanadin mutuwar wani matashi mai suna Zakari Suleman a layin Barraakari, da ke Bagobiri unguwar Hausawa. Lamarin ya auku  ne ranar Asabar da karfe biyar da rabi na safe bayan kammala sallar Asuba ranar da aka tafka ruwan sama kamar da bakin masaki, sai babbar wayar wutar lantarki ta katse […]

Wayar lantarki ta halaka dan agaji

Wayar wutar lantarki ta yi sanadin mutuwar wani matashi mai suna Zakari Suleman a layin Barraakari, da ke Bagobiri unguwar Hausawa.

Lamarin ya auku  ne ranar Asabar da karfe biyar da rabi na safe bayan kammala sallar Asuba ranar da aka tafka ruwan sama kamar da bakin masaki, sai babbar wayar wutar lantarki ta katse ta fado kasa ragowar, wadda ta fada kan gidan makwaftansa sai gobara ta kama, inda ihun a kawo dauki ne ya jawo hankalin marigayi Zakari ya fito daga dakinsa domin kashe gobara, kamar yadda Babangida Umar Kwamandan Kungiyar Agaji ta Fityanul Islam da ke layin Bagobiri Kalaba ya shaida wa Aminiya cewa: “Ihun a kawo dauki na gobarar da ta kama makwaftansa ce ta sanya ya zabura ya zuba ruwa a bokiti ya kada sabulun omo ya fita waje don kashe wutar, bai sani ba ashe daya daga cikin wayar da ta yanke ta fado daga sama na nan a kasa, kuma da wutar lantarki jikinta ya fita kafa ba takalmi, sai ya taka wayar ba tare da ya sani ba,  nan take wutar ta kama shi ta kone masa kafafuwa ya fadi. “ A cewarsa, Marigayin dan asalin kauyen Kanwa-Yola ta Karamar Hukumar Madobi  da ke Jihar Kano ya mutu yabar da guda .

Kuma wakilin mu ya tuntubi Alhaji Salisu Abba Lawan Sarkin Hausawan Kalaba kan jin korafin da zai yi ga gwamnati dangane da wannan lamari sai ya ce: “Ina kira ga gwamnati da ta sanya a sauya wayoyin wutar lantarki da ke babbar hanyar raba wuta, domin wasu daga cikinsu sun shafe sama da shekara 40. Sun riga sun tsufa suna bukatar a sake su.”

Kafin rasuwarsa daya ne daga cikin manyan kungiyar agaji ta Fitiyanul Islam a Kalaba ne, kuma yana sana’ar musayar kudin kasashen ketare. Mamacin ya samu shaida tagari a wurin jama’ar gari da kuma ta wadanda suka yi ma’amala ko huldar kasuwanci da shi. Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda adinin Musulunci ya tanadar.