Wayar salula ta haddasa mutuwar sojojin Rasha 89 a Ukraine
Ta lashi takobin hukunta jami’an da aka samu da sakaci har suka janyo mutuwar sojojin.
Rundunar Sojin Rasha ta ce, akwai yiwuwar sojojinta sun yi amfani ne da wayoyin salula wadanda suka bai wa takwarorinsu na Ukraine damar gano matsuguninsu har suka kai musu farmakin da ya kashe 89 daga cikinsu.
Sai dai tuni Rashawa suka fara mayar wa da rundunar sojin martani da suka ce, ta fadi haka ne domin wanke kanta daga zargin sakaci.
- China na yi wa Duniya nuku-nuku kan alkaluman Coronavirus —WHO
- Sarkin dawa: Dabbar da ake jin gurnaninta daga nisan mil 5
Hatta masharhanta da ke goyon bayan shugaba Vladimir Putin sun ce, watakila ma adadin sojojin da suka mutun ya zarta 89.
Asarar sojoji 89, ita ce mafi girma da Rasha ta ce ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Ukraine a cikin watan Fabairun bara.
Sojojin na Rasha sun mutu ne sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar musu a Makiivka da ke yankin gabashin Ukraine, inda Rasha ta mamaye.
Gwamnatin Rasha ta ce, hukumominta na gudanar da bincike domin fayyace ainihin abin da ya faru, sannan sun lashi takobin hukunta jami’an da aka samu da sakaci har suka janyo mutuwar sojojin.