Wayar wutar lantarki ta kona mutum 6 kurmus a Filato
Wutar ta tashi ne lokacin da mutanen ke tsaka da barci
Akalla mutum shida sun kone kurmus a Jos, babban birnin Jihar Filato bayan wata gobara da ta tashi sakamakon fadowar wayar wutar lantarki.
Aminiya ta gano cewa, wayar, wacce ta fado daga babban layin dakon lantarki a yankin Kabong na birnin na Jos ta kuma jikkawa wasu mutane da dama sannan ta kone shaguna.
Lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 2:00 na daren Juma’a, lokacin da mutanen suke tsaka da sharar barci.
Wani shugaban matasa a yankin, Sylvanus Boniface, ya ce gobarar ta faru ne bayan wata wayar babban layin ta fado a kan wata wayar, inda suka hadu kuma wutar ta tashi.
Ya shaida wa wakilinmu cewa daga cikin wadanda suka mutun har da wasu mutum biyu ’yan uwan juna, kuma yanzu haka suna dakin adana gawarwaki, yayin da wadanda suka ji raunuka daban-daban kuma aka garzaya da su asibitocin Ola da ECWA Jankwano.
Sylvanus ya ce shi kansa da kyar ya sha daga gobarar lokacin da ya tashi ya kashe hasken da ke dakinsa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Alabo Alfred, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya umarci DPOn yankin da ya tattauna da mazauna wajen da lamarin ya faru.
Ya kuma shawarci jama’a da su ci gaba da daukar matakan kariya ta hanyar karkashe kayayyakin lantarki lokacin da za su tashi daga shagunansu.