Wayo bai sayar da taba sai yajinta
Abin farin ciki ne yadda Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Dokta Ibe Kachukwu ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya za ta samar da wasu madudan kudi kafin darshen wannan shekara don fara ayyukan hado man fetur da iskar gas da aka ce an gano su jibge a Arewacin dasar nan. Duk da cewa wannan ba sabon […]
Abin farin ciki ne yadda Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Dokta Ibe Kachukwu ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya za ta samar da wasu madudan kudi kafin darshen wannan shekara don fara ayyukan hado man fetur da iskar gas da aka ce an gano su jibge a Arewacin dasar nan. Duk da cewa wannan ba sabon labari ne ba ga al’ummomin Arewa, amma duk da haka nan abin farin ciki ne a ji cewa a yanzu gwamnati da gaske take yi dangane da haka. Wahalar neman albarkatun man fetur a jihohin Arewacin dasar nan ya fi hadilon bidar allura a cikin ruwa.
Amma burin ganin an kai ga biyan budata game da haka bai zame a banza ba, domin kuwa a wurare da yawa an samu burbushin man, an kuma fahimci cewa, hada za ta cimma ruwa idan an dudufa sosai wajen tonowa. Dangane da haka an ce an samu albarkatu masu tarin yawa a gabar Tafkin Chadi, wanda ya yi iyaka da dasashen Kamaru da Chadi. Haka nan kuma an tabbatar akwai irin wadannan albarkatun a gabar kogin Komadugu Yobe, a dukkan wuraren da ya kurda ta Jihar Yobe, ya gangara cikin Tafkin Chadi. Dangane da haka ne ma aka samu man a yankin dasar Nijar da ke iyaka da Arewacin Jihar Yobe.
To ba wadannan wuraren ne kadai Allah Ya tarfa wa garinsu nono ba, a jihohin Bauchi ma da Gombe an gano dimbin albarkatun man, an kuma hadidance akwai shi a gabar Kogin Binuwai. A ’yan shekarun baya ma an gano arzikin man fetur kwance a wani yankin Kudu-maso Gabashin Jihar Kogi, aka kuma fahimci cewa, Jihar Sakkwato na zaune ne dirshan bisa irin wannnan albarkar.
Amma a duk lokacin da aka ce an gano albarkatun mai a wani yanki na Arewa sai abin ya zame tamkar labarin danzon kurege ga hukumomin Gwamnatin Tarayya, wadanda tono man da sarrafa shi ya dogara a wuyansu. A gabannin darewar mulkin Gwamna Ibrahim Idris na Jihar Kogi, an gano dimbin arzikin man fetur kwance a jiharsa, ya kuma gayyato dwararrun masana harkokin hadar mai, sun kuma tabbatar da haka, amma ba wani abin da aka yi don daukar matakan amfana da shi. Baicin haka nan kuma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Magatakarda Wammako, ya taba tabbatar da cewa, dwararru da manema albarkatun dardashin dasa sun yi dacen samun danyen man fetur a jiharsa. Amma baicin yayata wannan batun da ’yan jarida suka yi, babu wani jami’in Gwamnatin Tarayya ko na kwamfanonin da suka gano man fetur din da ya yi darin haske game da haka. Haka nan kuma an dade ana cewa akwai albarkatun man fetur a Jihar Bauchi da Gombe, duk a yankin Arewa-maso-Gabashin dasar nan.
Kafin dai a fahimci cewa an gano albarkatun man fetur a wani bangare na shiyyar Gabashin dasar nan, an dade da samun bayanai game da dacewar da aka yi da wannan baiwa a jihohin Arewacin dasar nan da yawa, amma gwamnati ba ta nuna ta san da haka ba. Tun da dai a shiyyoyin Arewaci ne aka gano albarkatun mai, ai ba za a fada ba, kuma babu wani dalilin da zai sa a tashi haidan don tonowa, tun da dai ba daunar yankin ake da arziki ba. Amma da yake ana son yi wa Arewa rinton albarkatun man da Buwayi Ya huwace mata sai aka ce wai man da aka gano a Jihar Kogi ma na Jihar Anambra ne.
Wannan al’amari ne mai rikitarwa, kuma Gwamnatin Tarayya ta di ta ce uffan game da da’awar da Jihar Kogi ke yi cewa, arzikin man da Jihar Anambra ke tundaho da shi a jiharta aka samu, kuma rashin daukar matakan gaggawa don bin bahasin tadaddamar da ta biyo baya game da haka na iya haddasa gagarumar rigima tsakanin al’ummomin jihohin Anambra da na Kogi, domin kuwa a wancan lokacin tsohon Shugaba Goodluck Jonthan ya kai ziyara a Jihar Anambra, ya kuma tabbatar musu da cewa man na jihar ne, sa’annan ya umurci a sanya ta a cikin jihohin da ke da arzikin man fetur a Najeriya.
Idan kuma aka koma kan batun din mayar da hankalin Gwamnatin Tarayya game da rashin fara ayyukan hadowa da sarrafa dimbin albarkatun man da aka gano a wurare da yawa a yankin Arewa, sai a fahimci cewa ba a budatar Arewa ne da daruwa da wannan arzikin. Manya-manyan dasashen Yammaci da Gabashin duniya sun kallafa ransu bisa wannan arzikin, kuma a saboda haka ne ake ta bullo da take-taken da suka haddasa yamutsi da rashin kwanciyar hankali a duk inda ake cewa an samu arzikin man fetur a yankin Arewa-maso-Gabashin dasar nan wadanda suka yi iyaka da sassan da aka samu man fetur a dasashen madwabta, kamar su Nijar da Chadi. Rige-rigen da suke yi don yin kaka-gida, su ji dadin tatsar wannan arziki a jihohin Barno da Yobe ne ke jawo fitintinun da ke wakana a wuraren, ana kuma jingina su da addini.
Kowa dai ya san cewa akwai albarkatun man fetur a Arewa-maso-Gabashin dasar nan, Gwamnatin Tarayya ma da kanta, da kuma kamfanin NNDC na raya yankunan Arewa, sun bayar da kudi don bincikowa, an kai ga ganowa, amma an di turzawa don fara hadowa. To ga shi nan ta bari al’amarin ya jawo wa al’ummomin yankin bala’i tun kafin su fara cin moriyarsa, kamar yadda man fetur ya zame wa dasar jangwam. Idan har da gaske gwamnati ke yi game da hanzarta binciken gabar kogunan dasar da ke kan iyakokin dasashe madwabta, musamman ma a Arewa, don gano albarkatun man fetur, to sai ta fara da inda aka tabbatar mata cewa akwai dimbin albarkatun da aka di tonowa, domin an ce wayo bai sayar da taba, sai yajinta.