Wayon ’Yar Gwari

Wata ’yar Gwari ce mahaifiyarta ta aike ta sawo robobi a Jos. Dama duk mako akan sawo mata robobin domin tana sayarwa, amma rannan sai wanda ya saba sawo mata baya nan, shi ya sa ta aiki ‘yarta da kudi domin ta sawo mata. Suna cikin tafiya a mota sai ’yan fashi suka tare su, […]

Wayon ’Yar Gwari
Wayon ’Yar Gwari

Wata ’yar Gwari ce mahaifiyarta ta aike ta sawo robobi a Jos. Dama duk mako akan sawo mata robobin domin tana sayarwa, amma rannan sai wanda ya saba sawo mata baya nan, shi ya sa ta aiki ‘yarta da kudi domin ta sawo mata. Suna cikin tafiya a mota sai ’yan fashi suka tare su, suka ce kowa ya fito da kudin da ke hannunsa ya mika. Da suka zo kan ’yar Gwari, aka ce ta kawo kudi, sai ta fito da kudi kashi biyu, ta ce: “Dama mamata ta ce mini idan na same ku a hanya, in ba ku wannan.” Ta mika masu Naira hamsin. Sannan ta nuna musu tulin kudi masu yawa a daya hannun, ta ce: “Wannan kuwa, mama ta ce in boye su da kyau, kada in nuna muku, in je Jos in sawo mata robobi.”
Daga Umar Abaji Zamau 08037494622