Wayoyi biliyan 5 za su zama bola a 2022 —Rahoto

Manyan wayoyi na daga cikin kayayyakin laturoni da muka fi maida hankali a kansu.

Wayoyi biliyan 5 za su zama bola a 2022 —Rahoto

Masana sun ce sama da biliyan biyar daga cikin wayoyin salula biliyan 16 da aka yi kiyasin ana da su a fadin duniya za su zama tarkace a 2022.

Rahoton ya nuna duk da cewa wayoyin na dauke da wasu muhimman abubuwa da za a iya sake sarrafa su don amfani, amma haka za a yi watsi da su wanda hakan ka iya barazana ga lafiyar al’umma da muhalli.

Daya daga cikin masanan, Pascal Leroy ya ce, “Manyan wayoyi na daga cikin kayayyakin laturoni da muka fi maida hankali a kansu.

“Idan ba mu sarrafa  kayayyakin cikinsu muka saka yi amfani da su ba, dole za mu rika zuwa mu nemo su a kasashe irin su China da Congo,” in ji shi.

Wayoyin da lamarin ya shafa wani dan kaso ne daga tarkacen kayayyaki lanturoni na ton miliyan 44.48 da ake yi duk shekara kamar yadda rahoto ya nuna.

Ya ce, wannan na faruwa ne yayin da mutane suka manta ko suka zabi ajiye wayoyin da suka lalace ko suka daina amfani da su a wurare daban-daban maimakon su mika su wajen gyara, ko kuma inda za a iya tattara a kwashe su zuwa kamfani domin sake sarrafa su.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos