Wazirin Katsina ya ajiye rawaninsa
Furucin da Waziri Lugga ya yi kan matsalar tsaro ya tayar da kura.
Rahotanni sun bayyana cewa, Wazirin Katsina na biyar da ya fito daga gidan Sarautar Sullubawa, Alhaji Sani Abubakar Lugga, ya ajiye rawaninsa a ranar Alhamis.
Aminiya ta tabbatar da hakan daga bakin mai magana da yawun masaurautar Katsina, Mallam Iro Bindawa.
- ’Yan ta’adda sun hallaka matafiya 18 a Nijar
- Kasuwannin duniya sun tafka asara bayan Rasha ta shiga Ukraine da yaki
Majiyar Katsina City News ta ce hakan na zuwa ne a sakamakon takaddamar da ta biyo bayan wani jawabi da Wazirin ya gabatar a Ilorin, babban Jihar Kwara a kan matsalar tsaro da kasar nan ke ciki baki daya.
Bayanai sun ce a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin na Ilorin inda aka yi masa tambayoyi a kan yanayin tsaro da Jihar Katsina ke ciki kuma Alhaji Lugga ya ba da bayanin kusan duk abin da manyan Katsina kan furta.
Wannan jawabin nasa, wanda wasu jaridun kasar nan suka dauka a ranar Litinin da ta gabata, ya harzuka masarautar Katsina, lamarin da ya sanya ta rubuta masa takardar tuhuma don neman ya ba da bayani a kan dalilin furucin da ya yi.
A bayanin nasa da ya rubuta, Alhaji Sani Lugga ya ba da hujjojinsa na cewa akwai matsalar tsaro a Katsina har ta shafi Kananan Hukumomi takwas da hujjarsa ta cewa an rufe makarantu kuma wasu Hakimai har sun yi kaura daga masarautunsu.
A ranar Alhamis Wazirin na Katsina ya ba da amsa cikakkiya mai shafuka hudu da kwararran hujjoji har da maganganun Gwamnan Katsina, Sarkin Katsina da Sakataren Gwamnatin Jihar.
Kazalika, Alhaji Lugga ya aika wa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardarsa ta ajiye sarautarsa.
A wasikar da ya rubuta mai shafuka biyu, ya kawo tarihin sarautar gidansu ta Kanem Bakashe da ke kasar Nijar, wadda ta samo asali tun 1579.
Kazalika ya kawo tarihin sarautar Waziri a gidansu, wadda ta fara tun 1906. Ya kuma ba da bayanin yadda aka nada shi Wazirin Katsina a 2002, wanda ya ce a yau Alhamis, 24 ga watan Fabrairun 2022 ya ajiye.
Haka kuma ya yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Katsina tare da neman gafararsa idan har hukuncin da ya dauka ya sosa masa rai.