WHO ta nemi hadin-gwiwa don ci gaban Arewa maso Gabas

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira kan a  samar da hadin gwiwar cibiyoyin kudi da ke sassan duniya wajen ciyar da yankin Arewa maso Gabas. Wannan kiran ya fito ne daga bakin Daraktar Hukumar Lafiyar Sashen Afirka, Dakta Matshidiso Moeti a tsakiyar wannan wata, inda ta ce yankin a halin yanzu yana cikin […]

WHO ta nemi hadin-gwiwa don ci gaban Arewa maso Gabas

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira kan a  samar da hadin gwiwar cibiyoyin kudi da ke sassan duniya wajen ciyar da yankin Arewa maso Gabas.

Wannan kiran ya fito ne daga bakin Daraktar Hukumar Lafiyar Sashen Afirka, Dakta Matshidiso Moeti a tsakiyar wannan wata, inda ta ce yankin a halin yanzu yana cikin wani yanayin dake bukatar gaggauta ayyukan sake gina shi. Haka kuma ayyukan jinkai na bukatar biyo bayan sake gina yankin ne.

Ta ce amma aiwatar da hakan na bukatar gagarumin hadin gwiwa da manyan cibiyoyi irin su Babban Bankin Duniya da Babban Bankin Cigaban Afirka da sauran manyan masu bada tallafi wadanda suke da rajin cigaban al’umma wajen samar da kyakkyawan sakamakon da zai sake maida yankin cikin kwanciyar hankali.

Hakazalika Dakta Moeti, ta bayyana damuwarta game da tsarin tallafin lafiyar dake gudana a yankin, inda ta ce akwai bukatar WHO ta kara tallafawa wajen magance zazzabin cizon saura, wanda ke ci gaba da zama babban hadari a Najeriya.

Ta kara da cewa hukumar lafiyar za ta taiamaka wa gwamnatin tarayya wajen samar da karin magunguna, gidan sauro da kuma maganin feshi sannan ta karfafa harkokin lafiyar a madadin agajinta ga gwamnatin wajen samar da cibiyoyin lafiya a Arewa maso Gabas.

“Akwai kimanin mutane kusan miliyan 5 da ake sa ran tallafin hukumar ta (WHO) din zai kai gare su. Sannan hukumar za ta cigaba da tallafawa yaki da cizon sauro a dukkan sassan Najeriya.”

A yayin maida jawabinsa, Ministan Lafiya na Najeriya, Farfesa Isaac Adewole ya bayyana cewa shirye-shiryen Hukumar Lafiya ta Duniyar (WHO), na ci gaba da wanzuwa a dukkan sassar kasar nan sannan kuma ya godewa hukumar bisa tallafin da ta ke bayarwa.