WHO ta tallafa wa yara 6,000 da abinci mai gina jiki a Borno

An raba wa iyaye mata da sauran masu kula da yara tallafin a kananan hukumomi 11 da ke Borno.

WHO ta tallafa wa yara 6,000 da abinci mai gina jiki a Borno

Borno

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bai wa yara 6,000 masu fama da matsananciyar yunwa tallafin abinci mai gina jiki.

Da take gabatar da kayayyakin ga bangarorin kiwon  lafiya, Manajar Kula da Ayyukan Gaggawa na WHO, Dokta Beatrice Muraguri, ta bayyana cewa, “an raba tallafin ne domin shawo kan kalubalen rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a cikin al’ummomin da rikicin ta’addanci ya shafa a Jihar Borno.”

Ta ba da tabbacin cewa tallafin ya isa ga yaran da aka yi niyya da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Da yake karbar tallafin, Babban Sakatare na Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jin kai, wanda Darakta a ma’aikatar, Adamu Usman ya wakilta, ya gode wa hukumar ta WHO bisa tallafin domin  yaki da rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara.

Ya tabbatar wa Dokta Muraguri cewa za a raba wa iyaye mata da sauran masu kulawa da yara a kananan hukumomi 11 da ke jihar ta Borno.

Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Maiduguri Metropolitan Council (MMC), Jere, Konduga, Gwoza, Bama, Uba/Askira, Kaga, Gubio, Monguno, Damboa da Mobbar, da kuma wasu al’mmomin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.