Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja
Daga cikin mutum 568 waɗanda lamarin ya shafa har da Gwamnan Imo, Hope Uzodinma da na Bayelsa, Diri Douye.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙwace filayen wasu jiga-jigan ’yan siyasa da suka haɗa da gwamnoni da sanatoci a babban birnin ƙasar.
Daga cikin mutum 568 waɗanda lamarin ya shafa har da Gwamnan Imo, Hope Uzodinma da takwaransa na Bayelsa, Diri Douye da kuma Sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa waɗanda suka mallaki filaye a unguwar Maitama II da Cadastral Zone A10 da ke Abuja.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ministan, Lere Olayinka ya fitar, ya ce ƙwace filayen na zuwa ne bayan cikar wa’adin makonni biyu na biyan shaidar haƙƙin mallakar filayen ta C of O a Turance.
Sauran mashahurai da ke cikin jerin mutum 568 da aka ƙwacewa filayen sun haɗa da tsohon Gwamnan Enugu, Chimaroke Nnamani da Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa, Abba Moro, da Shugabar Hukuma Kula da ’yan Nijeriya mazauna ƙetare, Abike Dabiri-Erewa da wasu ’yan Majalisar Tarayya.
Ana iya tuna cewa, tun a watan Oktoban bara ne Wike ya bai wa aƙalla mutum 3,273 wa’adin makonni biyu su biya kuɗin shaidar haƙƙin mallakar filayen inda daga ciki 2,511 suka amsa wannan umarni.
Sai dai bayan cikar wa’adin, Ministan ya ƙara sabunta wa’adin ga ragowar masu filaye 762 da ba su biya kuɗin ba, amma har zuwa ranar 15 ga watan Janairun nan, masu filaye 194 ne suka cika umarnin yayin da ragowar 568 suka yi biris da shi.